- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 930–586 BC
The Divided Kingdom
The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sarakuna 22:7kusan 642 K.H.
Amma ba sa bukata su ba da bayanin kuɗin da aka danƙa musu domin suna aikinsu da aminci.”
- 2 Sarakuna 22:8kusan 642 K.H.
Hilkiya babban firist ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan, shi kuma ya karanta.
- 2 Sarakuna 22:9kusan 642 K.H.
Sa’an nan Shafan ya koma wurin sarki ya ce masa, “Hafsoshinka sun kwashe kuɗin da suke a haikalin Ubangiji, suka ba wa masu aiki da masu lura da haikalin.”
- 2 Sarakuna 22:10kusan 642 K.H.
Sa’an nan Shafan magatakarda ya ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta shi a gaban sarki.
- 2 Sarakuna 22:11kusan 642 K.H.
Da sarki ya ji kalmomin Littafin Doka, sai ya kece tufafinsa.
- 2 Sarakuna 22:12kusan 642 K.H.
Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikahiya, da Shafan magatakarda, da kuma Asahiya mai hidimar sarki, ya ce,
- 2 Sarakuna 22:13kusan 642 K.H.
“Ku je, ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da saboda jama’a da kuma saboda dukan Yahuda game da abin da wannan littafi da aka samo ya ƙunsa. Fushin Ubangiji mai girma ne a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye kalmomin littafin nan ba; ba su aikata bisa ga abin da yake a rubuce game da mu ba.”
- 2 Sarakuna 22:14kusan 642 K.H.
Sai Hilkiya firist, da Ahikam, Akbor, da Shafan, da kuma Asahiya suka je don su yi magana da annabiya Hulda, matan Shallum ɗan Tikba, ɗan Harhas, mai ajiyar tufafi. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.
- 2 Sarakuna 22:15kusan 642 K.H.
Sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ku faɗa wa mutumin da ya aike ku wurina,
- 2 Sarakuna 22:16kusan 642 K.H.
‘Ga abin da Ubangiji ya ce, zan kawo masifa wa wannan wuri da kuma wa kan mutanen wurin, bisa ga dukan abubuwan da suke a rubuce a cikin littafin da sarkin Yahuda ya karanta.
- 2 Sarakuna 22:17kusan 642 K.H.
Domin sun yashe ni suka ƙona turare wa waɗansu alloli, suka tozarta ni da dukan gumakan da hannuwansu suka sassaƙa, fushina zai yi ƙuna a kan wannan wuri, ba kuwa zai huce ba.’
- 2 Sarakuna 22:18kusan 642 K.H.
Ku faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aike ku ku nemi nufin Ubangiji, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa game da kalmomin da ka ji.
- 2 Sarakuna 22:19kusan 642 K.H.
Domin zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Ubangiji sa’ad da ka ji abin da na faɗa game da wannan wuri da mutanen wurin, cewa za su zama la’antattu da kuma kango, domin kuma ka kece tufafinka, ka kuma yi kuka a gabana, na ji ka, in ji Ubangiji.
- 2 Sarakuna 22:20kusan 642 K.H.
Saboda haka zan haɗa ka da kakanninka, za a kuma binne ka cikin salama. Idanunka kuma ba za su ga dukan wannan masifan da zan jawo wa wurin nan ba.’ ” Sai suka kai wa sarki abin da ta faɗa.
Sai sarki ya kira dukan dattawan Yahuda da Urushalima.
Sai ya haura zuwa cikin haikalin Ubangiji tare da mutanen Yahuda, da na Urushalima, da firistoci, da annabawa, dukan mutane, manya da ƙanana. Ya karanta musu duk kalmomin Littafin Alkawari, wanda aka samu a haikalin Ubangiji.
Sarki ya tsaya dab da ginshiƙi ya kuma sabunta alkawarin a gaban Ubangiji, ya ce zai bi Ubangiji, yă kiyaye dokokinsa, da ƙa’idodinsa, da farillansa, da dukan zuciyarsa da dukan ransa, ta haka ya tabbatar da kalmomin alkawarin da yake a rubuce a cikin littafin nan. Sa’an nan dukan mutane ma suka yi alkawari yin haka.
Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel.
Ya kawar da firistocin gumakan da sarakunan Yahuda suka naɗa don su ƙona turare a masujadan kan tuddai na garuruwan Yahuda, da kuma waɗanda suke kewaye da Urushalima, masu ƙona turare wa Ba’al, rana da wata, ga rukunin taurari, da kuma ga dukan rundunan taurari.
Ya ɗauke ginshiƙin Ashera daga haikalin Ubangiji zuwa Kwarin Kidron can bayan Urushalima, ya ƙone shi a can. Ya niƙa shi sai da ya zama toka, sai ya watsar da ƙurar a filin kabarin talakawa.
Ya kuma rurrushe mazaunan karuwai mazan haikali waɗanda suke a haikalin Ubangiji, da kuma inda mata suke yi wa Ashera saƙa.
Yosiya ya kawo dukan firistoci daga garuruwan Yahuda, ya kuma lalatar da masujadan kan tuddai daga Geba har zuwa Beyersheba, inda firistoci suke ƙona turare. Ya rurrushe matsafai a ƙofofi shigan gari na mashigi zuwa Ƙofar Yoshuwa, gwamnan birnin, wanda yake a hagu da ƙofar birnin.
Ko da yake firistocin masujadan kan tuddai ba su yi hidima a bagaden Ubangiji a Urushalima ba, sun ci burodi marar yisti tare da sauran firistoci.
Ya lalatar da Tofet, wanda yake a Kwarin Ben Hinnom, don kada kowa yă iya yin amfani da wurin don yă miƙa hadayar ɗansa, ko ’yarsa a wuta ga Molek.
Ya kawar da dawakan nan da sarakunan Yahuda suka keɓe wa gumakan nan na rana daga mashigin haikalin Ubangiji. Waɗannan dawakan suna kusa da ɗakin Natan Melek, ɗaya daga cikin dattawan sarki. Yosiya ya kuma ƙone kekunan yaƙi a yin sujada ga gumakan nan rana.