Tsallake zuwa abun ciki

circa 930–586 BC

The Divided Kingdom

The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.

1,722 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 2 Sarakuna 20:4kusan 713 K.H.

    Kafin Ishaya yă bar tsakiyar filin gida, sai maganar Ubangiji ta zo masa cewa,

  2. 2 Sarakuna 20:5kusan 713 K.H.

    “Ka koma ka ce wa Hezekiya, shugaban mutanena, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na mahaifinka Dawuda ya ce, na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan warkar da kai. A rana ta uku daga yau za ka haura zuwa haikalin Ubangiji.

  3. 2 Sarakuna 20:6kusan 713 K.H.

    Zan ƙara maka shekara goma sha biyar. Zan kuma cece ka daga hannun sarkin Assuriya. Zan kāre birnin nan saboda kaina da kuma bawana Dawuda.’ ”

  4. 2 Sarakuna 20:7kusan 713 K.H.

    Sai Ishaya ya ce, “A kwaɓa ɓaure.” Sai aka yi haka, aka shafa wa marurun, ya kuma warke.

  5. 2 Sarakuna 20:8kusan 713 K.H.

    Hezekiya ya tambayi Ishaya, “Wace alama ce za tă nuna cewa Ubangiji zai warkar da ni, kuma cewa in tafi haikalin Ubangiji kwana uku daga yanzu?”

  6. 2 Sarakuna 20:9kusan 713 K.H.

    Sai Ishaya ya ce, “Ga alamar Ubangiji zuwa gare ka da za tă nuna cewa Ubangiji zai cika alkawarinsa. Kana so inuwa tă yi gaba da taki goma, ko tă koma baya da taki goma?”

  7. 2 Sarakuna 20:10kusan 713 K.H.

    “Ai, abu mai sauƙi ne inuwa tă yi gaba da taki goma.” In ji Hezekiya, “Gwamma dai tă koma baya da taki goma.”

  8. 2 Sarakuna 20:11kusan 713 K.H.

    Sai annabi Ishaya ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa inuwa ta koma baya da taki goma bisa ga magwajin rana wanda Sarki Ahaz ya gina.

  9. 2 Sarakuna 20:12kusan 712 K.H.

    A wannan lokaci, Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu tare da kyauta, domin ya sami labarin rashin lafiyar Hezekiya.

  10. 2 Sarakuna 20:13kusan 712 K.H.

    Hezekiya ya karɓi jakadun, ya nuna musu dukan abin da yake a ɗakunan ajiyarsa, azurfa, zinariya, kayan ƙanshi da mai, wurin ajiye makamansa da kuma dukan abin da aka samu a ɗakin ajiyarsa. Babu wani abu a fadansa ko a dukan mulkinsa da Hezekiya bai nuna musu ba.

  11. 2 Sarakuna 20:14kusan 712 K.H.

    Sai annabi Ishaya ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya tambaye shi ya ce, “Me mutanen nan suka ce, kuma daga ina suka fito?” Sai Hezekiya ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Daga Babilon.”

  12. 2 Sarakuna 20:15kusan 712 K.H.

    Annabin ya yi tambaya, “Me suka gani a fadanka?” Hezekiya ya ce, “Ba abin da yake a ma’ajina da ban nuna musu ba.”

  13. 2 Sarakuna 20:16kusan 712 K.H.

    Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji kalmar Ubangiji.

  14. 2 Sarakuna 20:17kusan 712 K.H.

    Lokaci yana zuwa da za a kwashe kome a fadanka da kuma dukan abubuwan da kakanninka suka tara har yă zuwa yau, a kai su Babilon. Ba abin da za a rage, in ji Ubangiji.

  15. 2 Sarakuna 20:18kusan 712 K.H.

    Za a kuma kwashe waɗansu daga cikin zuriyarka, na jiki da jininka waɗanda za a haifa maka, su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.”

  16. 2 Sarakuna 20:19kusan 712 K.H.

    Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka faɗa ta yi kyau.” Gama ya yi tunani cewa, “Ai, ba ni da damuwa, tun da yake za a yi zaman lafiya da salama a kwanakina.”

  17. 2 Sarakuna 20:20kusan 712 K.H.

    Game da sauran ayyukan mulkin Hezekiya, dukan nasarorinsa da yadda ya yi tafki da kuma bututun ruwa inda ya kawo ruwa cikin birni, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

  18. 2 Sarakuna 20:21kusan 698 K.H.

    Hezekiya ya huta tare da kakanninsa. Manasse ɗansa kuma ya gāje shi.

  19. 2 Sarakuna 21:1kusan 698 K.H.

    Manasse yana da shekara goma sha biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara hamsin da biyar a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hefziba.

  20. 2 Sarakuna 21:2kusan 698 K.H.

    Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya bi munanan al’adun al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.

  21. 2 Sarakuna 21:3kusan 698 K.H.

    Ya sāke gina masujadan da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai. Ya kafa ginshiƙin Ashera kamar yadda Ahab sarkin Isra’ila ya yi. Ya durƙusa wa dukan rundunan taurari ya yi musu sujada.

  22. 2 Sarakuna 21:4kusan 698 K.H.

    Ya gina bagadai a haikalin Ubangiji, wurin da Ubangiji ya ce, “A Urushalima ne zan sa Sunana.”

  23. 2 Sarakuna 21:5kusan 698 K.H.

    Cikin filaye biyu na haikalin Ubangiji kuwa, ya gina bagadai na dukan rundunan taurari.

  24. 2 Sarakuna 21:6kusan 683 K.H.

    Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.

  25. 2 Sarakuna 21:7kusan 698 K.H.

    Ya ɗauki siffar ginshiƙin Asherar da ya yi, ya sa a haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Solomon, “A cikin wannan haikali, da kuma cikin Urushalima inda na zaɓa daga kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.