Tsallake zuwa abun ciki

circa 930–586 BC

The Divided Kingdom

The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.

1,722 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 2 Sarakuna 5:5kusan 894 K.H.

    Sarkin Aram ya ce, “Ko ta ƙaƙa, ka tafi, zan aika da wasiƙa ga sarkin Isra’ila.” Sai Na’aman ya tashi, ɗauke da talenti goma na azurfa, shekel dubu shida na zinariya, da tufafi kashi goma.

  2. 2 Sarakuna 5:6kusan 894 K.H.

    Wasiƙar da ya kai wa sarkin Isra’ila ta ce, “Da wannan wasiƙa ina aika Na’aman gare ka don ka warkar da kuturtarsa.”

  3. 2 Sarakuna 5:7kusan 894 K.H.

    Da sarkin Isra’ila ya karanta wasiƙar, sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne? Zan iya ɗauke rai ko in mai da shi? Me ya sa wannan mutum ya turo mini wannan mutum in warkar da kuturtarsa? Dubi fa yadda yake nemana da faɗa!”

  4. 2 Sarakuna 5:8kusan 894 K.H.

    Da Elisha mutumin Allah ya ji cewa sarkin Isra’ila ya yayyage tufafinsa, sai ya aika masa da wannan saƙo, “Don me za ka yayyage tufafinka? Ka sa mutumin yă zo wurina, zai kuwa san cewa akwai annabi a Isra’ila.”

  5. 2 Sarakuna 5:9kusan 894 K.H.

    Saboda haka Na’aman ya tafi da dawakansa da keken yaƙinsa, ya tsaya a ƙofar gidan Elisha.

  6. 2 Sarakuna 5:10kusan 894 K.H.

    Sai Elisha ya aika ’yan saƙo su ce masa, “Je, ka nutse sau bakwai a Urdun, fatar jikinka za tă koma daidai, ka kuma tsarkaka.”

  7. 2 Sarakuna 5:11kusan 894 K.H.

    Amma Na’aman ya tashi daga can da fushi yana cewa, “Na yi tsammani zai fito ne wurina yă tsaya, yă yi kira bisa ga sunan Ubangiji Allahnsa, yă kaɗa hannunsa inda kuturtar take, yă warkar da ni.

  8. 2 Sarakuna 5:12kusan 894 K.H.

    Ashe, Amana da Farfa, kogunan da suke Damaskus, ba su fi dukan ruwan da suke Isra’ila ba? Me zai sa ba zan nutse cikinsu in tsarkaka ba?” Sai ya juya ya yi tafiyarsa da fushi.

  9. 2 Sarakuna 5:13kusan 894 K.H.

    Sai bayin Na’aman suka je kusa da shi suka ce, “Baba, da a ce annabin ya ce ka yi wani abu mai wuya, da ba za ka yi ba? Balle fa cewa kawai ya yi, ‘Ka yi wanka ka kuma tsarkaka’!”

  10. 2 Sarakuna 5:14kusan 894 K.H.

    Saboda haka Na’aman ya je ya nutse sau bakwai a Urdun, yadda mutumin Allah ya ce masa, sai fatarsa ta koma kamar ta ɗan yaro.

  11. 2 Sarakuna 5:15kusan 894 K.H.

    Sai Na’aman da dukan masu hidimarsa suka koma wurin mutumin Allah. Na’aman ya tsaya a gaban mutumin Allah ya ce, “Yanzu na san cewa babu wani Allah a duk duniya sai a Isra’ila. Ina roƙonka ka karɓi kyauta daga hannun bawanka.”

  12. 2 Sarakuna 5:16kusan 894 K.H.

    Annabin ya amsa ya ce, “Muddin Ubangiji wanda nake bauta masa yana a raye, ba zan karɓi kome ba.” Ko da yake Na’aman ya yi ta roƙonsa, amma ya ƙi.

  13. 2 Sarakuna 5:17kusan 894 K.H.

    Sai Na’aman ya ce, “In ba za ka karɓa ba, ina roƙonka, bari a ba wa bawanka ƙasa gwargwadon abin da jakuna biyu za su iya ɗauka, gama bawanka ba zai sāke yin hadaya ta ƙonawa, ko wata hadaya ga wani allah ba, sai ga Ubangiji.

  14. 2 Sarakuna 5:18kusan 894 K.H.

    Amma ina fata Ubangiji zai gafarta wa bawanka saboda abu guda. Bari yă gafarta mini sa’ad da na raka sarkina zuwa haikalin Rimmon domin yă yi sujada, bari Ubangiji yă yi wa bawanka gafara saboda wannan.”

  15. 2 Sarakuna 5:19kusan 894 K.H.

    Sai Elisha ya ce, “Ka sauka lafiya.” Bayan Na’aman ya yi ɗan nisa,

  16. 2 Sarakuna 5:20kusan 894 K.H.

    sai Gehazi, bawan Elisha mutumin Allah, ya yi tunani a ransa ya ce, “Maigidana ya yi wa Na’aman mutumin Aram nan ƙaramci da bai karɓi duk abin da ya kawo ba. Muddin Ubangiji yana a raye, zan bi shi a guje in karɓi wani abu daga gare shi.”

  17. 2 Sarakuna 5:21kusan 894 K.H.

    Saboda haka Gehazi ya bi Na’aman a guje. Da Na’aman ya hango shi yana zuwa a guje, sai ya sauka daga keken yaƙinsa ya tarye shi ya ce, “Lafiya?”

  18. 2 Sarakuna 5:22kusan 894 K.H.

    Gehazi ya amsa ya ce, “Lafiya ƙalau. Maigidana ne ya aiko ni cewa, ‘Samari biyu daga ƙungiyar annabawa sun ziyarce ni daga ƙasa mai duwatsu na yankin Efraim. Ina roƙonka ka ba su talenti na azurfa da tufafi kashi biyu.’ ”

  19. 2 Sarakuna 5:23kusan 894 K.H.

    Na’aman ya ce, “Ba damuwa, karɓi talenti biyu.” Ya roƙi Gehazi yă karɓa, sa’an nan ya ƙunsa masa talentin biyu na azurfa ya sa masa a kan jakankuna biyu, ya haɗa da tufafi kashi biyu, ya ba bayinsa biyu suka ɗauka, ya ce su sha gaban Gehazi.

  20. 2 Sarakuna 5:24kusan 894 K.H.

    Da Gehazi ya isa wani tudu, sai ya karɓi kayan daga wurin bayin ya shiga da su a ɓoye a cikin gida. Sa’an nan ya sallami mutanen suka tafi.

  21. 2 Sarakuna 5:25kusan 894 K.H.

    Sa’an nan ya shiga ya tsaya a gaban maigidansa Elisha. Sai Elisha ya tambaye shi ya ce, “Ina ka je, Gehazi?” Sai Gehazi ya amsa ya ce, “Bawanka bai je ko’ina ba.”

  22. 2 Sarakuna 5:26kusan 894 K.H.

    Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba sa’ad da mutumin ya sauko daga keken yaƙinsa ya tarye ka. Kana gani wannan lokaci ne da za a karɓi kuɗi, da riguna, da gonar inabi, da tumaki, da bijimai, da bayi maza da mata?

  23. 2 Sarakuna 5:27kusan 894 K.H.

    Kuturtar Na’aman zai manne maka da zuriyarka har abada.” Sai Gehazi ya fita daga gaban Elisha a kuturce, fari fat kamar dusar ƙanƙara.

  24. 2 Sarakuna 6:1kusan 893 K.H.

    Sai ƙungiyar annabawa suka ce wa Elisha, “Duba, wurin da muke taruwa ya kāsa mana.

  25. 2 Sarakuna 6:2kusan 893 K.H.

    Bari mu je Urdun, inda kowannenmu zai saro itace; mu gina inda za mu zauna.” Sai ya ce musu, “Ku je.”