- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Jonathan
Ayoyin da suka ambaci Jonathan
Yonatan ya tashi daga tebur cin abincin da fushi. A rana ta biyun kuwa bai ci abinci ba, gama yana baƙin ciki game da rashin kunyar mahaifinsa game da Dawuda.
Da safe Yonatan ya tafi domin yă sadu da Dawuda a fili. Ya tafi tare da wani ƙaramin yaro.
Da yaron ya isa wurin da kibiyan Yonatan ya fāɗi, Yonatan ya kira shi ya ce, “Kibiyan na gabanka fa.”
Sai ya tā da murya ya ce, “Maza, yi sauri kada ka tsaya.” Yaron ya ɗauko kibiya ya kawo wa maigidansa.
(Yaron kuwa bai san kome game da wannan abu ba, sai Yonatan da Dawuda kawai.)
Yonatan ya ba wa yaron makaman ya ce, “Ka ɗauka ka koma gari.”
Yonatan ya ce wa Dawuda, “Sauka lafiya, mun riga mun yi rantsuwar abokantaka da juna a cikin sunan Ubangiji cewa, ‘Ubangiji ne shaida tsakanina da kai, tsakanin zuriyarka da zuriyata har abada.’ ” Sai Dawuda ya tafi, Yonatan kuwa ya koma gari.
Yonatan ɗan Shawulu kuwa ya tafi wurin Dawuda a Horesh, ya ƙarfafa shi yă dogara ga Allah.
Su biyunsu kuwa suka ɗaura yarjejjeniya a gaban Ubangiji. Sai Yonatan ya koma gida amma Dawuda ya zauna Horesh.
Filistiyawa suka abka wa Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kashe ’ya’yan Shawulu. Yonatan da Abinadab da Malki-Shuwa.
Dawuda ya ce, “Gaya mini, me ya faru?” Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga yaƙi, aka kuma karkashe yawancin mutane. Shawulu da ɗansa Yonatan ma sun mutu.”
Sai Dawuda ya ce wa saurayin da ya kawo labarin, “Yaya ka san cewa Shawulu da ɗansa Yonatan sun mutu?”
Suka yi makoki, da kuka, da azumi har yamma saboda Shawulu da ɗansa Yonatan, da saboda sojojin Ubangiji, da kuma gidan Isra’ila, gama an karkashe su a yaƙi.
Dawuda ya rera wannan makoki saboda Shawulu da ɗansa Yonatan.
“Daga jinin waɗanda aka kashe, daga tsokar naman jarumi, bakan Yonatan bai juye baya ba, takobin Shawulu bai komo ba tare da gamsuwa ba.
Shawulu da Yonatan, a raye ƙaunatattu ne da kuma bansha’awa, a mace kuma ba su rabu ba. Sun fi gaggafa sauri, sun fi zaki ƙarfi.
“Jarumawa sun fāɗi a yaƙi! Ga Yonatan matacce a tuddanku.
Na yi baƙin ciki saboda kai, Yonatan ɗan’uwana; ƙaunatacce kake a gare ni. Ƙaunarka a gare ni abar al’ajabi ce, abar al’ajabi fiye da ta mace.
(Yonatan ɗan Shawulu yana da ɗa mai suna Mefiboshet wanda yake gurgu a duka ƙafafu. Yana da shekara biyar ne sa’ad da labarin mutuwar Shawulu da Yonatan ya zo daga Yezireyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi ta gudu, amma yayinda take hanzari tă gudu, sai ya fāɗo, ya gurgunce.)
Wata rana Dawuda ya yi tambaya ya ce, “Akwai wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu wanda zan nuna masa alheri saboda Yonatan?”
Sa’an nan sarki ya yi tambaya ya ce, “Babu wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu don in nuna masa alherin Allah?” Ziba ya ce wa sarki, “Har yanzu akwai ɗan Yonatan da ya rage, sai dai shi gurgu ne a dukan ƙafafu.”
Sa’ad da Mefiboshet ɗan Yonatan, ɗan Shawulu, ya zo wurin Dawuda, sai ya rusuna har ƙasa ya yi gaisuwar bangirma. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, ga ni, bawanka.”
Dawuda ya ce, “Kada ka ji tsoro, gama tabbatacce zan nuna maka alheri saboda mahaifinka Yonatan. Zan mayar maka da dukan ƙasar da take ta kakanka Shawulu, kullum kuma za ka ci a teburina.”
Sarki ya ware Mefiboshet ɗan Yonatan jikan Shawulu, saboda rantsuwar da take tsakanin Dawuda da Yonatan, ɗan Shawulu a gaban Ubangiji.
sai ya je ya kwashe ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan daga mutanen Yabesh Gileyad (Gama mutanen sun saci gawawwakin Shawulu da Yonatan daga inda Filistiyawa suka kakkafa su a kan itace a filin Bet-Shan, bayan da Filistiyawa suka kashe su a Gilbowa.)