Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da Yaƙub ya farka daga barci, sai ya yi tunani ya ce, “Tabbatacce Ubangiji yana a wannan wuri, ban kuwa sani ba.”

  2. Kashegari da sassafe, sai Yaƙub ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuma zuba mai a kansa.

  3. Sa’an nan Yaƙub ya yi alkawari cewa, “In Allah zai kasance tare da ni yă kuma lura da ni a wannan tafiya, yă kuma ba ni abinci in ci da tufafi in sa,

  4. Sa’an nan Yaƙub ya ci gaba da tafiyarsa har ya kai ƙasar mutanen gabashi.

  5. Yaƙub ya tambayi makiyayan ya ce, “’Yan’uwa, ina kuka fito?” Suka amsa, “Mu daga Haran ne.”

  6. Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila ’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa.

  7. Sa’an nan Yaƙub ya sumbaci Rahila, ya kuma ɗaga murya ya yi kuka.

  8. Ya riga ya faɗa wa Rahila cewa shi dangin mahaifinta ne kuma ɗan Rebeka. Saboda haka ta ruga da gudu ta faɗa wa mahaifinta.

  9. Nan da nan, da Laban ya sami labari game da Yaƙub, ɗan ’yar’uwarsa, ya gaggauta yă sadu da shi. Sai ya rungume shi ya sumbace shi, ya kuma kawo shi gidansa, a can kuwa Yaƙub ya faɗa masa dukan waɗannan abubuwa.

  10. sai Laban ya ce masa, “Don kawai kai dangina ne na kusa, sai kawai ka yi mini aiki a banza? Faɗa mini abin da albashinka zai zama.”

  11. Yaƙub ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, “Zan yi maka aiki na shekaru bakwai domin ƙaramar ’yarka Rahila.”

  12. Saboda haka Yaƙub ya yi bauta shekaru bakwai domin a ba shi Rahila, amma shekarun suka zama kamar ’yan kwanaki ne kawai gare shi saboda ƙaunar da yake mata.

  13. Sa’an nan Yaƙub ya ce wa Laban, “Ba ni matata. Lokacina ya cika, ina kuma so in kwana da ita.”

  14. Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi ’yarsa Rahila tă zama matarsa.

  15. Sa’ad da Rahila ta ga cewa ba tă haifa wa Yaƙub ’ya’ya ba, sai ta fara kishin ’yar’uwarta. Saboda haka ta ce wa Yaƙub, “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!”

  16. Yaƙub ya fusata da ita ya ce, “Ina a matsayin Allah ne wanda ya hana ke samun ’ya’ya?”

  17. Saboda haka ta ba shi baranyarta Bilha tă zama matarsa. Yaƙub kuwa ya kwana da ita,

  18. ta kuwa yi ciki, ta kuma haifi ɗa.

  19. Baranyar Rahila ta sāke yin ciki ta kuma haifi wa Yaƙub ɗa na biyu.

  20. Sa’ad da Liyatu ta ga cewa ta daina haihuwa, sai ta ɗauki mai hidimarta Zilfa ta ba da ita ga Yaƙub tă zama matarsa.

  21. Baranyar Liyatu, Zilfa ta haifa wa Yaƙub ɗa.

  22. Zilfa baranyar Liyatu ta haifa wa Yaƙub ɗa na biyu.

  23. Saboda haka sa’ad da Yaƙub ya dawo daga jeji a wannan yamma sai Liyatu ta fito ta tarye shi. Ta ce, “Dole ka kwana da ni, na yi hayarka da manta-uwa na ɗana.” Saboda haka ya kwana da ita a wannan dare.

  24. Allah ya saurari Liyatu, ta kuwa yi ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na biyar.

  25. Liyatu ta sāke yin ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na shida.