God
Ayoyin da suka ambaci God
Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai mayar da ku masu arziki ƙwarai a cikin dukan aiki hannuwanku, da kuma cikin ’ya’yanku, da ’ya’yan shanunku, da kuma hatsin gonarku. Ubangiji zai sāke jin daɗinku yă sa ku yi arziki, kamar dai yadda ya ji daɗin kakanninku.
In dai kuka yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma kiyaye umarnansa da ƙa’idodin da aka rubuta a wannan Littafin Doka, kuka juyo ga Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.
Gama na umarce ku a yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, don ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma dokokinsa, sa’an nan za ku rayu, ku kuma ƙaru, Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a ƙasar da kuke shiga don ci gādonta.
don kuma ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku saurari muryarsa, ku kuma manne masa. Gama Ubangiji shi ranku, zai kuwa ba ku shekaru masu yawa a ƙasar da ya rantse zai ba wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.
“Yanzu shekaruna ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji ya ce mini, ‘Ba za ka haye Urdun ba.’
Ubangiji Allahnku kansa zai haye a gabanku. Zai hallaka waɗannan al’ummai da suke gabanku, za ku kuwa mallaki ƙasarsu. Yoshuwa shi ma zai haye a gabanku, yadda Ubangiji ya faɗa.
Ubangiji zai yi da su, yadda ya yi da Sihon da Og, sarakunan Amoriyawa, waɗanda ya hallaka tare da ƙasarsu.
Ubangiji zai bashe su gare ku, dole kuma ku yi musu dukan abin da na umarce ku.
Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
Sai Musa ya kira Yoshuwa, ya ce masa a gaban dukan Isra’ila, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama dole ka tafi tare da mutanen nan zuwa cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse cewa za ba wa kakanninku, dole kuma ka raba ta gare su ta zama gādonsu.
Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”
Sai Musa ya rubuta wannan doka ya kuma ba da ita ga firistoci, ’ya’yan Lawi maza, waɗanda sukan ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji, da kuma dukan dattawan Isra’ila.
sa’ad da dukan Isra’ila suka zo, don su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa, za ku karanta wannan doka a gabansu, a kunnuwansu.
Ku tattara mutane, maza, mata da kuma yara, da baƙin da suke zama a cikin garuruwanku, saboda su saurara, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su lura, su bi dukan kalmomin wannan doka.
’Ya’yansu, waɗanda ba su san wannan doka ba, dole su ji ta, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku muddin ranku a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.”
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu ranar mutuwarka ta yi kusa. Ka kira Yoshuwa, ku shigo Tentin Sujada, inda zan ba shi ragamar aiki.” Saboda haka Musa da Yoshuwa suka zo, suka kuma shiga Tentin Sujada.
Ubangiji kuwa ya bayyana a Tentin Sujada a cikin ginshiƙin girgije, sai girgijen ya tsaya a ƙofar Tentin Sujada.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Za ka huta tare da kakanninka, waɗannan mutane kuwa ba da daɗewa ba za su yi karuwanci ga baƙin alloli na ƙasar da za su shiga. Za su yashe ni su kuma karya alkawarin da na yi da su.
A wannan rana zan yi fushi da su, in kuma yashe su; zan ɓoye fuskata daga gare su, za a kuwa hallaka su. Masifu masu yawa da wahaloli masu yawa za su auka musu, a wannan rana kuwa za su ce, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu’
Tabbatacce kuwa, zan ɓoye musu fuskata saboda muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka.
“To, sai ka rubuta wannan waƙa domin kanka, ka koya wa Isra’ilawa, ka kuma sa su rera ta, don tă zama shaida a kansu.
Sa’ad da na kawo su cikin ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa ga kakanninsu, sa’ad da kuma suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba, za su juya ga waɗansu alloli su bauta musu, su ƙi ni, su kuma karya alkawarina.
Sa’ad da kuma masifu masu yawa da wahaloli masu yawa suka auko musu, wannan waƙa za tă zama shaida a kansu, domin zuriyarsu ba za tă manta da ita ba. Na san abin da za su iya yi, kafin ma in kawo su cikin ƙasar da na yi musu alkawari da rantsuwa.”
Ubangiji ya ba wa Yoshuwa ɗan Nun wannan umarni, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama za ka kawo Isra’ilawa cikin ƙasar da na yi musu alkawari da rantsuwa, ni kaina kuwa zan kasance tare da kai.”
sai ya ba wa Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji wannan umarni,