Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji zai shari’anta mutanensa yă kuma ji tausayin bayinsa sa’ad da ya ga ƙarfinsu ya ƙare babu kowa kuma da ya rage, bawa ko ’yantacce.

  2. Zai ce, “To, ina allolinsu, dutsen da suka yi mafaka a ciki,

  3. “Ku duba yanzu cewa ni ne Shi! Ba wani allah in ban da ni. Nakan kashe in kuma rayar, nakan sa rauni in kuma warkar, ba wanda yake da iko yă cece wani daga hannuna.

  4. Na ɗaga hannu sama na kuma furta. Muddin ina raye har abada,

  5. sa’ad da na wasa takobi mai walƙiya hannuna kuwa ya cafke shi don yin hukunci, zan ɗau fansa a kan abokan gābana in sāka wa waɗanda suke ƙina.

  6. Zan sa kibiyoyina su bugu da jini, yayinda takobina yana cin nama, jinin kisassu da na kamammu, kawunan shugabannin abokan gāba.”

  7. Ku yi farin ciki, ya ku al’ummai, tare da mutanensa, gama zai rama ɗau fansar jinin bayinsa; zai ɗau fansa a kan abokan gābansa yă kuma yi kafara domin ƙasarsa da mutanensa.

  8. A wannan rana Ubangiji ya ce wa Musa,

  9. “Ka hau Duwatsun Abarim zuwa Dutsen Nebo a Mowab, tsallake daga Yeriko, ka hangi Kan’ana, ƙasar da nake ba wa Isra’ilawa gādo.

  10. Wannan kuwa domin ku biyu kun fid da aminci gare ni a gaban Isra’ilawa a ruwan Meriba ta Kadesh, a Hamadar Zin kuma saboda ba ku riƙe tsarkina a cikin Isra’ilawa ba.

  11. Saboda haka, za ka ga ƙasar daga nesa kawai; ba za ka shiga ƙasar da nake ba wa mutanen Isra’ila ba.”

  12. Wannan ita ce albarkar da Musa mutumin Allah ya furta a kan Isra’ilawa, kafin yă rasu.

  13. Ya ce, “Ubangiji ya zo daga Sinai ya haskaka a bisansu daga Seyir; ya haskaka daga Dutsen Faran. Ya zo tare da dubban tsarkakansa daga kudu, daga gangara dutsensa.

  14. Tabbatacce kai ne wanda yake ƙaunar mutane; dukan tsarkaka suna a hannunka. A ƙafafunka, duk suka rusuna, daga wurinka kuma suka karɓi umarni,

  15. Shi ne sarki a bisa Yeshurun sa’ad da shugabannin mutane suka taru, tare da kabilan Isra’ila.

  16. Ya kuma faɗa wannan game da Yahuda, “Ka ji, ya Ubangiji, kukan Yahuda; ka kawo shi wurin mutanensa. Da hannuwansa ya kāre kansa. Ka taimake shi a kan maƙiyansa!”

  17. Game da Lawi ya ce, “Tummim da Urim na mutumin da ka nuna masa tagomashi ne. Ka gwada shi a Massa; ka yi faɗa da shi a ruwan Meriba.

  18. Ya yi zancen mahaifinsa da mahaifiyarsa ya ce, ‘Ban kula da su ba.’ Bai gane da ’yan’uwansa ba, ko yă yarda da ’ya’yansa, amma ya kiyaye maganarka ya tsare alkawarinka.

  19. Ya koyar da farillanka ga Yaƙub, dokarka kuma ga Isra’ila. Ya miƙa turare a gabanka da kuma hadaya ta ƙonawa ɗungum a kan bagadenka.

  20. Ka albarkaci ɗaukan dabarunsa, ya Ubangiji, ka kuma ji daɗin aikin hannuwansa. Ka murƙushe kwankwaso waɗanda suka tayar masa; ka bugi abokan gābansa har sai ba su ƙara tashi ba.”

  21. Game da Benyamin ya ce, “Bari ƙaunataccen Ubangiji yă zauna lafiya kusa da shi, gama yana tsare shi dukan yini, wanda kuma Ubangiji yake ƙauna yana zama a tsakanin kafaɗunsa.”

  22. Game da Yusuf ya ce, “Bari Ubangiji yă albarkaci ƙasarsa da raɓa mai daraja daga sama a bisa da kuma zurfin ruwan da suke kwance a ƙarƙashi;

  23. Tare da kyautai mafi kyau na duniya da cikarta, da tagomashi na wanda yake zama a ƙaramin itace mai ƙonewa. Bari duk waɗannan su zauna a kan Yusuf, a goshin sarki a cikin ’yan’uwansa.

  24. Ya zaɓi ƙasa mafi kyau wa kansa; aka ajiye masa rabon shugaba. Sa’ad da shugabannin mutane suka taru, ya aikata adalcin Ubangiji da kuma hukuncinsa game da Isra’ila.”

  25. Game da Naftali ya ce, “Naftali ƙosasshe ne da tagomashin Ubangiji, ya kuma cika albarkarsa; zai gāji gefen kudu zuwa tafki.”