Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Yanzu ina roƙonku ku rantse mini da Ubangiji cewa za ku yi wa iyalina alheri kamar yadda na yi muku alheri. Ku ba ni ƙwaƙƙwarar shaida cewa

  2. Mutanen suka tabbatar mata suka ce, “Ranmu a bakin ranki! In ba ki faɗa wa kowa abin da ya kawo mu ba, za mu yi miki alheri da aminci lokacin da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”

  3. Suka ce wa Yoshuwa, “Ba shakka Ubangiji ya ba mu ƙasan nan duka, tana hannunmu, mutane can duk sun narke da tsoro saboda mu.”

  4. ba da umarni ga mutane, suna cewa, “Lokacin da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, da firistoci waɗanda su ne Lawiyawa, suna ɗauke da shi, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi.

  5. Yoshuwa ya ce wa mutane, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai yi abubuwan al’ajabi a cikinku.”

  6. Ubangiji kuwa ya ce wa Yoshuwa, “Yau, zan fara ɗaukaka ka a gaban Isra’ilawa duka don su sani cewa ina tare da kai kamar yadda na kasance tare da Musa.

  7. Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Ku zo nan ku ji maganar Ubangiji Allahnku.

  8. Ta haka ne za ku san cewa Allah mai rai yana tare da ku, kuma ba shakka a gabanku za ku gani zai kore Kan’aniyawa, Hittiyawa, Hiwiyawa, Ferizziyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa da Yebusiyawa.

  9. Ku duba, akwatin alkawarin Ubangiji na dukan duniya zai yi gaba cikin Urdun kafin ku.

  10. Kuma da firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangiji dukan duniya, sun sa ƙafa cikin ruwan kogin Urdun, ruwan da yake gudu a rafin zai tsaya cik yă taru a wuri ɗaya.”

  11. Firistocin kuwa da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya daram a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Urdun a lokacin da Isra’ilawa suka ƙetarewa, har sai da dukan mutane suka gama ƙetarewa.

  12. Da al’umma gaba ɗaya suka ƙetare Urdun, Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,

  13. ya ce musu, “Ku je tsakiyar Urdun inda akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku yake. Kowannenku yă ɗauki dutse ɗaya a kafaɗarsa, bisa ga yawan kabilan Isra’ila,

  14. Sai ku ce musu, ruwan Urdun ya yanke a gaban akwatin alkawari na Ubangiji, a lokacin da akwatin alkawarin ya ƙetare Urdun. Waɗannan duwatsu za su zama abin tuni ga Isra’ilawa har abada.”

  15. Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Yoshuwa ya umarce su. Suka ɗauki duwatsu guda goma sha biyu bisa ga yawan kabilan Isra’ila, yadda Ubangiji ya gaya wa Yoshuwa; suka tafi da su masauƙinsu, a can suka ajiye su.

  16. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Yoshuwa yă gaya wa mutane, kamar yadda Musa ya ce Yoshuwa yă yi. Mutanen suka wuce da sauri.

  17. Sai da dukan mutanen suka wuce sa’an nan akwatin alkawari da firistoci suka sha gaba.

  18. Wajen mutum dubu arba’in shirye domin yaƙi, suka wuce a gaban Ubangiji zuwa filayen Yeriko.

  19. A ranan nan Ubangiji ya ɗaukaka Yoshuwa a gaban Isra’ilawa; suka kuma ba shi girma dukan kwanakin ransa, kamar yadda suka girmama Musa.

  20. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,

  21. Firistocin kuwa suka fito daga kogin ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji. Nan da nan da ƙafafunsu suka taɓa busasshiyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya gangaro ya cika kogin kamar yadda yake a dā.

  22. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya yanke a gabanku, har sai da kuka gama wucewa, kamar yadda ya yi a Jan Teku, a lokacin da ya busar da shi a gabanmu har sai da muka gama wucewa.

  23. Ya yi wannan ne domin dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji mai iko ne, domin kuma ku zama masu tsoron Ubangiji Allahnku.”

  24. To, da dukan sarakunan Amoriyawa na yammancin Urdun, da dukan sarakunan Kan’aniyawan da suke bakin teku suka ji yadda Ubangiji ya busar da kogin Urdun a gaban Isra’ilawa, har sai da dukansu suka ƙetare, zuciyarsu ta narke, suka karaya sosai har ma suka rasa samun ƙarfin hali su fuskanci Isra’ilawa.

  25. A lokacin nan Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka yi wuƙaƙe na duwatsu ka yi wa Isra’ilawa kaciya.”