Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. “Babu wani kamar Allah na Yeshurun, wanda yake hawa a bisa sammai don yă taimake ka a kan gizagizai kuma a cikin darajarsa.

  2. Allah madawwami shi ne mafakarka, a ƙarƙashina kuma madawwamin hannuwa ne. Zai kore abokin gābanka a gabanka, yana cewa, ‘Ka hallaka shi!’

  3. Haka Isra’ila zai zauna lafiya shi kaɗai; zuriyar Yaƙub a tsare a ƙasar hatsi da sabon ruwan inabi, inda sammai za su zuba raɓa.

  4. Kai mai albarka ne, ya Isra’ila! Wane ne yake kamar ka, mutanen da Ubangiji ya ceta? Shi ne mafakarka da mai taimakonka da kuma takobinka mai ɗaukaka. Abokan gābanka za su zo neman jinƙai a gabanka, za ka kuwa tattake masujadansu.”

  5. Sai Musa ya hau Dutsen Nebo daga filayen Mowab, zuwa ƙwanƙolin Fisga, wanda yake ƙetare Yeriko. A can Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, daga Gileyad zuwa Dan,

  6. Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, “Wannan ce ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, sa’ad da na ce, ‘Zan ba da ita ga zuriyarku.’ Na bar ka ka gani da idanunka, amma ba za ka haye zuwa cikinta ba.”

  7. Nan fa, a ƙasar Mowab Musa bawan Ubangiji ya mutu, yadda Ubangiji ya faɗa.

  8. Aka binne shi a Mowab, a kwarin kusa da Bet-Feyor, amma har wa yau babu wanda ya san inda kabarinsa yake.

  9. To, Yoshuwa ɗan Nun ya cika da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya hannuwansa a kansa. Saboda haka Isra’ilawa suka saurare shi, suka kuma aikata abin da Ubangiji ya umarci Musa.

  10. Tun daga nan ba a sāke yin wani annabi a Isra’ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska,

  11. wanda kuma ya yi dukan waɗannan alamu banmamaki da al’ajaban da Ubangiji ya aike shi yă yi a Masar, da a kan Fir’auna, da a kan dukan shugabanninsa, da kuma a kan dukan ƙasarsa.

  12. Bayan mutuwar Musa bawan Ubangiji, sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa ɗan Nun, mataimakin Musa,

  13. “Bawana Musa ya mutu. Yanzu sai ka tashi tare da mutanen nan duka, ku yi shirin ƙetare kogin Urdun zuwa cikin ƙasar da zan ba su Isra’ilawa.

  14. Zan ba ku duk ƙasar da za ku taka, kamar yadda na yi wa Musa alkawari.

  15. Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.

  16. “Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su.

  17. Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je.

  18. Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”

  19. “Ku ratsa cikin sansani, ku gaya wa mutane, ‘Ku shirya guzurinku. Nan da kwana uku za ku ƙetare Urdun a nan, don ku je ka mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ta zama taku.’ ”

  20. “Ku tuna da umarnin da Musa bawan Ubangiji ya yi muku. ‘Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa, ya kuma ba ku wannan ƙasa.’

  21. har sai lokacin da Ubangiji ya ba su hutawa, kamar yadda ya yi muku, kuma har sai su ma sun ƙwace ƙasar da Ubangiji Allahnku ya yi alkawari zai ba su. Bayan haka ne za ku koma ku mallaki ƙasarku, wadda Musa bawan Ubangiji ya ba ku a gabashin Urdun.”

  22. Kamar yadda muka yi wa Musa biyayya, haka za mu yi maka biyayya. Ubangiji Allahnka ya kasance tare da Musa.

  23. ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya riga ya ba ku ƙasan nan, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku.

  24. Mun ji yadda Ubangiji ya busar da ruwan Jan Teku domin ku lokacin da kuka fito daga ƙasar Masar, da kuma abin da kuka yi wa Sihon da Og, sarakunan nan biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, waɗanda kuka hallaka su sarai.

  25. Da muka ji labarin, duk sai zuciyar kowa ta narke, kowa ya karaya saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne Allah na sama da ƙasa.