Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. “Tafi babban birnin nan Ninebe ka yi mata wa’azi, saboda muguntarta ta haura zuwa gabana.”

  2. Amma Yunana ya gudu daga Ubangiji ya nufi Tarshish. Ya gangara zuwa Yaffa, inda ya sami jirgin ruwa mai shirin tashi daga tashar. Bayan ya biya kuɗin tafiya, sai ya shiga jirgi ya kama hanya zuwa Tarshish don yă tsere wa Ubangiji.

  3. Sai Ubangiji ya aika da babban iska a bisan teku, hadiri ya tsananta ƙwarai har jirgin ya yi barazanar farfashewa.

  4. Sai kyaftin ɗin ya je wajensa ya ce masa, “Don me kake barci? Tashi ka kira bisa ga allahnka! Mai yiwuwa yă ji mu, yă cece mu don kada mu hallaka.”

  5. Sai ya amsa, “Ni mutumin Ibraniyawa ne, ina kuma bauta wa Ubangiji Allah na sama, wanda ya yi teku da tuddai.”

  6. Sai matuƙan jirgin suka tsorata ƙwarai, suka ce masa, “Wane irin mugun abu ne ka aikata haka?” (Sun gane cewa yana gudu ne daga wurin Ubangiji, domin ya riga ya faɗa musu.)

  7. Sai suka yi kuka ga Ubangiji suka ce, “Ya Ubangiji, in ka yarda kada ka bar mu mu mutu saboda ran mutumin nan. Kada ka yi mana hukuncin masu kisankai, gama kai ne, ya Ubangiji, ka ga ya gamshe ka.”

  8. Ganin haka sai mutanen suka cika da tsoron Ubangiji, suka kuma miƙa wa Ubangiji hadaya, suka yi wa’adi da shi.

  9. Amma Ubangiji ya tanada wani babban kifi da zai haɗiye Yunana, Yunana kuwa ya yi yini uku da dare uku a ciki cikin kifin.

  10. Daga ciki cikin kifi, Yunana ya yi addu’a ga Ubangiji Allahnsa.

  11. Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata.

  12. Cikin tashin hankali, ka jefa ni cikin zurfafa, a tsakiyar teku, ka kuma jujjuya ni a cikin ruwa; dukan raƙuman ruwanka da ambaliyarka sun bi ta kaina.

  13. Sai na ce, ‘An kore ni daga fuskarka; duk da haka zan sāke duba wajen haikalinka mai tsarki.’

  14. Na nutsa har ƙarƙashin tuddai; a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada. Amma ka dawo da raina daga rami, Ya Ubangiji Allahna.

  15. “Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni, na tuna da kai ya Ubangiji, addu’ata kuma ta kai gare ka, a haikalinka mai tsarki.

  16. Amma ni, da waƙar godiya, zan miƙa tawa hadaya gare ka. Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi. Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.”

  17. Sai Ubangiji ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunana a gaɓan teku.

  18. Sa’an nan sai maganar Ubangiji ta zo wa Yunana sau na biyu.

  19. “Tafi babban birnin nan Ninebe, ka yi masa shelar saƙon da na ba ka.”

  20. Sai Yunana ya yi biyayya da maganar Ubangiji, ya tafi Ninebe. Ninebe birni ne da yake da muhimmanci, wanda sai an ɗauki kwana uku kafin a iya zaga shi.

  21. Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki.

  22. Bari kowane mutum da dabba yă yafa rigunan makoki. Kowa yă roƙi Allah da gaske, kowa kuma yă bar mugayen ayyukan da yake yi.

  23. Wa ya sani? Ko Allah zai ji tausayinmu da kuma juyayinmu yă janye zafin fushinsa don kada mu hallaka.”

  24. Da Allah ya ga abin da suka yi, da kuma yadda suka juya daga mugayen hanyoyinsu sai ya ji tausayinsu, bai kawo hallaka a kansu yadda ya yi shirin yi ba.

  25. Sai ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ba irin abin da na faɗa ke nan ba tun ina gida? Wannan ne ya sa na yi ƙoƙarin tserewa zuwa Tarshish. Ai, na sani kai Allah ne mai alheri da tausayi, mai jinkirin fushi da cikakkiyar ƙauna, kai Allah ne mai dakatar da nufinka na yin hukunci.