God
Ayoyin da suka ambaci God
Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,” in ji Ubangiji, wanda sunansa ne Allah Mai Iko.
Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta, “Ina ƙyamar girman kan Yaƙub, ba na kuma son kagarunsa; zan ba da birnin da duk abin da yake cikinta.”
In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.”
Gama Ubangiji ya ba da umarni, zai kuma ragargaza babban gidan nan kucu-kucu ƙaramin gidan kuwa zai yi rugu-rugu da shi.
Gama Ubangiji Allah Maɗaukaki ya ce, “Zan sa wata ƙasa ta tayar muku, ya ku gidan Isra’ila, wadda za tă matsa muku tun daga Lebo Hamat zuwa kwarin Araba.”
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji yana shirya cincirindon fāri bayan da aka ƙarasa yankan rabon hatsin da yake na sarki, hatsi na biyu kuma yake tohuwa.
Sa’ad da suka cinye kome, sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ka gafarta! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa. “Wannan ba zai faru ba,” in ji Ubangiji.
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji Mai Iko Duka yana shirin hukunta da wuta; wutar ta ƙone teku ta kuma ƙone ƙasa.
Sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ina roƙonka ka dakata! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa. “Wannan ma ba zai faru ba,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Ga abin da ya nuna mini. Ubangiji yana tsaye kusa da bangon da aka gina, bisa ga awon igiyar gwada gini, da kuma magwaji a hannunsa.
Sai Ubangiji ya tambaye ni, “Me kake gani, Amos?” Sai na amsa, “Igiyar gwada gini.” Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Duba, zan sa igiyan nan a cikin mutanena Isra’ila; ba zan ƙara barinsu ba.
“Za a hallakar da wuraren sujada na Ishaku kuma tsarkakan wurare na Isra’ila za su zama kango; da takobina zan tayar wa gidan Yerobowam.”
Amma Ubangiji ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’
Yanzu fa, sai ka ji maganar Ubangiji. Ka ce, “ ‘Kada in yi annabci a kan Isra’ila, kuma in daina yin wa’azi a kan gidan Ishaku.’
“Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “ ‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni, kuma da takobi za a kashe ’ya’yanka maza da mata. Za a auna ƙasarka a kuma raba ta, kai kuma za ka mutu a ƙasar arna. Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji ya nuna mini kwandon nunannun ’ya’yan itace.
Ya yi tambaya ya ce, “Me ka gani Amos?” Sai na amsa na ce, “Kwandon nunannun ’ya’yan itace.” Sai Ubangiji ya ce mini, “Lokaci ya yi wa mutanena Isra’ila da ba zan ƙara barinsu ba.
“A ranan nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “Waƙoƙin a haikali za su koma makoki. Za a ga gawawwaki a ko’ina! Shiru!”
Ubangiji ya rantse da Girman Yaƙub, “Ba zan taɓa mantawa da duk wani abin da suka yi ba.
“A wannan rana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “Zan sa rana ta fāɗi da tsakar rana in kuma duhunta duniya da rana tsaka.
Zan mai da bukukkuwanku na addini su zama makoki kuma dukan waƙoƙinku su zama kuka. Zan sa dukanku ku sa rigunan makoki za ku kuma aske kawunanku. Zan sa wannan lokaci yă zama kamar lokacin da ake makokin ɗan tilon da ake da shi kuma ƙarshenta kamar rana mai ɗaci.
“Ranakun suna zuwa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar, ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba, sai dai yunwa ta jin maganar Ubangiji.
Mutane za su yi ta tangaɗi daga teku zuwa teku suna yawo daga arewa zuwa kudu, suna neman maganar Ubangiji, amma ba za su samu ba.