Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Zan sa wuta a katangar Rabba da za tă ƙone kagarunta za a yi kururuwa a ranar yaƙi, faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.

  2. Sarkinta zai je bauta, shi da ma’aikatansa,” in ji Ubangiji.

  3. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Mowab, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama ya ƙone ƙasusuwan sarkin Edom suka zama sai ka ce toka.

  4. Zan sa wuta a Mowab da za tă ƙone kagarun Keriyot Mowab za tă gangara cikin hayaniya mai girma cikin kururuwar yaƙi da kuma ƙarar ƙaho.

  5. Zan hallaka mai mulkinta zan kuma kashe shugabanninta.”

  6. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Yahuda, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama sun ƙi bin dokar Ubangiji ba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba, domin allolin ƙarya sun ruɗe su, allolin da kakanninsu suka bauta.

  7. Zan sa wuta a Yahuda da za tă ƙone kagarun Urushalima.”

  8. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Isra’ila, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun sayar da adalai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.

  9. Sun tattake kawunan matalauta kamar yadda suke taka laka suka kuma danne wa marasa galihu gaskiya. Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda, suna kuma ɓata sunana mai tsarki.

  10. “Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu, ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul kuma mai ƙarfi kamar itacen oak. Na hallaka ’ya’yan itatuwansa daga sama, da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa.

  11. Na fitar da ku daga ƙasar Masar, na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada don in ba ku ƙasar Amoriyawa.

  12. “Na kuma tā da annabawa daga cikin ’ya’yanku maza waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku. Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?” In ji Ubangiji.

  13. “Saboda haka, yanzu zan murƙushe ku kamar yadda amalanke yakan murƙushe sa’ad da aka yi masa labtun hatsi.

  14. Ko jarumawa mafi jaruntaka za su gudu tsirara a ranan nan,” in ji Ubangiji.

  15. Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar.

  16. “Ku ne kaɗai na zaɓa cikin dukan al’umman duniya; saboda haka zan hukunta ku saboda dukan zunubanku.”

  17. Idan aka busa ƙaho a ciki birni mutane ba sa yin rawar jiki? Sa’ad da bala’i ya auko wa birni, ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba?

  18. Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.

  19. Zaki ya yi ruri, wa ba zai tsorata ba? Ubangiji Mai Iko Duka ya yi magana, wa ba zai yi annabci ba?

  20. “Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,” in ji Ubangiji, “sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.”

  21. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Abokin gāba zai ƙwace ƙasar, zai saukar da mafakarku, zai washe kagarunku.”

  22. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya, haka za a ceci Isra’ilawa, masu zama a Samariya da kan gado kawai da kuma a ɗan ƙyalle a kan dogayen kujerunsu.”

  23. “Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki.

  24. “A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta, zan hallaka bagadan Betel; za a yayyanka ƙahonin bagadan za su fāɗa ƙasa

  25. Zan rushe gidan rani da na damina; gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,” in ji Ubangiji.