Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. zan tattara dukan al’ummai in kuma kawo su Kwarin Yehoshafat Can zan yi musu shari’a game da gādona, mutanena Isra’ila, gama sun warwatsar da mutanena a cikin al’ummai sun kuma raba ƙasata.

  2. Sun jefa ƙuri’a a kan mutanena suna kuma sayar da yara maza don karuwanci, sun sayar da ’yan matan domin ruwan inabi wanda za su sha.

  3. “Yanzu mene ne damuwarku da ni, ya Taya da Sidon da kuma dukan mazaunan yankunan Filistiya? Kuna ƙoƙari ku sāka mini don abin da na yi ne? In kuna sāka mini ne, to, da gaggawa zan mayar muku da sakayya a kanku.

  4. Gama kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe dukiyata mafi kyau kun kai cikin haikalinku.

  5. “Duba, zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, in kuma yi muku abin da kuka yi musu.

  6. Zan sayar da ’ya’yanku maza da mata ga mutanen Yahuda, su kuma za su sayar da su ga mutanen Sabenawa, al’umma da take nesa da ku.” Ubangiji ya faɗa.

  7. Ku gaggauta, dukanku al’ummai daga kowane ɓangare, ku tattaru a can. Ka sauko da mayaƙanka, ya Ubangiji!

  8. “Bari a tā da dukan al’ummai; bari su kutsa zuwa Kwarin Yehoshafat gama a can zan zauna in shari’anta dukan al’ummai daga kowane ɓangare.

  9. Dubun dubbai suna a cikin kwarin yanke shawara! Gama ranar Ubangiji ta yi kusa a cikin kwarin yanke shawara.

  10. Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona tsawa kuma daga Urushalima; duniya da sararin sama za su yi rawan jiki. Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa, mafaka ga mutanensa Isra’ila.

  11. “Sa’an nan za ku san cewa ni, Ubangiji Allahnku, ina zaune a Sihiyona, dutsena mai tsarki. Urushalima za tă zama mai tsarki; baƙi ba za su ƙara mamaye ta ba.

  12. “A wannan rana duwatsu za su ɗiga da sabon ruwan inabi, tuddai kuma za su malmalo madara; dukan rafuffukan Yahuda za su yi ta gudano da ruwa. Maɓulɓula kuma za tă fito daga gidan Ubangiji haka ma ruwa a kwarin itatuwan ƙirya.

  13. Alhakin jininsu, wanda ban gafarta ba, zan gafarta.”

  14. Ya ce, “Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona ya kuma yi tsawa daga Urushalima; wuraren kiwo duk sun bushe, dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.”

  15. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Damaskus, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Domin sun ci zalunci Gileyad zalunci mai tsanani,

  16. zan sa wuta a gidan Hazayel, da za tă ƙona kagarun Ben-Hadad.

  17. Zan kakkarye ƙofofin Bet-Damaskus; zan hallaka sarkin da yake cikin Kwarin Awen da kuma mai riƙe da sandar mulkin Bet-Eden. Mutanen Aram za su je bauta a ƙasar Kir,” in ji Ubangiji.

  18. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Gaza, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun sayar wa Edom,

  19. Zan aika da wuta a katangar Gaza ta ƙone duk kagarunta.

  20. Zan hallaka sarkin Ashdod da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon. Zan hukunta Ekron, har sai dukan Filistiyawa sun mutu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  21. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Taya, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom, ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar ’yan’uwa ba,

  22. zan aika da wuta a Taya, da za tă ƙone kagarunta.”

  23. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Edom, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi, babu tausayi, domin ya ci gaba da fusata bai yarda yă huce daga fushinsa ba.

  24. Zan aika wuta a Teman da za tă ƙone kagarun Bozra.”

  25. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Ammon, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu don kawai yă ƙwace ƙasar.