God
Ayoyin da suka ambaci God
Yanzu, ya Ubangiji, ka ɗauki raina, domin ya fi sauƙi a gare ni in mutu da in rayu.”
Amma Ubangiji ya amsa, ya ce; “Daidai ne ka yi fushi?”
Sai Ubangiji Allah ya sa wata ’yar kuringa ta tsiro, ta yi girma a inda Yunana yake, don ta inuwantar da shi, yă ji daɗi. Yunana kuwa ya yi murna matuƙa da wannan kuringa.
Amma kashegari da safe sai Allah ya sa tsutsa ta cinye ’yar kuringar har ta mutu.
Sa’ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro, zafin ranar kuma ya buga kan Yunana, har ya ji sai ka ce zai suma. Ya so a ce ya mutu ma, sai ya ce, “Gara in mutu da a ce ina zaune da rai.”
Amma Allah ya ce wa Yunana, “Daidai ne ka yi fushi saboda wannan kuringa?” Sai Yunana ya ce, “I, daidai ne, ina fushi matuƙa, har ina so da na mutu ma.”
Sai Ubangiji ya ce, “Ai, wannan kuringa ta tsira dare ɗaya ta kuma ɓace kafin dare na biyu, ba ka yi wata wahala dominta ba, ba kai ne ka sa ta yi girma ba, duk da haka ranka ya ɓace saboda ita.
Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.
Ku ji, ya ku mutane duka, ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki, bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku, daga haikalinsa mai tsarki.
Duba! Ubangiji yana zuwa daga wurin zamansa; zai sauko yă taka maɗaukakan wuraren duniya.
Duwatsu za su narke a ƙarƙashin ƙafafunsa, kamar kaki a gaban wuta, kwaruruka kuma za su ɓace, kamar ruwan da yake gangarowa daga tsauni.
“Saboda haka zan mai da Samariya tarin juji, wurin noman inabi. Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari in kuma bar harsashin gininta a bayyane.
Za a ragargaje dukan allolinta; za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta; zan lalatar da dukan gumakanta. Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su, ga karuwanci kuma za su koma.”
Gama raunin Samariya ba mai warkewa ba ne; ya bazu har Yahuda. Ya ma kai bakin ƙofar mutanena, har ma Urushalima da kanta.
Mazaunan Marot sun ƙosa su ga alheri, amma Ubangiji ya sauko da azaba, har zuwa ƙofar Urushalima.
Ku mazaunan Maresha Ubangiji zai kawo wanda zai ci ku da yaƙi. Sarakunan Isra’ila za su gudu zuwa Adullam.
Saboda haka, Ubangiji ya ce, “Ina shirya wa waɗannan mutane bala’i, yadda ba za ku iya ceton kanku ba. Ba za ku ƙara tafiya kuna taƙama ba, gama zai zama lokacin bala’i ne.
A wannan rana mutane za su yi muku ba’a za su yi muku gwalo da wannan waƙar makoki, ‘An lalatar da mu sarai; an rarraba mallakar mutanena. Ya ɗauke shi daga gare ni! Ya miƙa filayenmu ga maciyan amanarmu.’ ”
Saboda haka ba za ku kasance da wani a taron jama’ar Ubangiji da zai raba ƙasar ta wurin jefa ƙuri’a ba.
Daidai ne a ce, ya gidan Yaƙub, “Ruhun Ubangiji yana fushi ne? Yana yin irin waɗannan abubuwa?” “Ashe, maganata ba tă amfane wanda ayyukansa suke daidai ba?
Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi kamar magabci. Kun tuɓe riga mai tsada daga waɗanda suke wucewa ba tare da kun damu ba, sai ka ce mutanen da suke komowa daga yaƙi.
Kun kori matan mutanena daga gidajensu masu daɗi. Kuka kawar da albarkata har abada daga wurin ’ya’yansu.
In maƙaryaci da mazambaci ya zo ya ce, ‘Zan yi muku annabci ku sami wadataccen ruwan inabi da barasa,’ zai dai zama annabin da ya dace da wannan mutane ne!
“Tabbatacce zan tattara ku duka, ya gidan Yaƙub; zan tattara ku raguwar Isra’ila. Zan kawo su wuri ɗaya kamar tumaki a cikin garke, kamar garke a wajen kiwonsa; wurin zai cika da mutane.
Wanda ya fasa ƙofa ya buɗe, shi zai haura yă yi musu jagora, za su fashe bangon su fita. Sarkinsu zai wuce gabansu, Ubangiji kuma zai kasance a gaba.”