Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. “Tsawon rabo na musamman da za ku bayar ga Ubangiji zai zama kamu 25,000, fāɗinsa kuma kamu 10,000.

  2. Wannan ne zai zama tsattsarkan rabo domin firistoci. Tsawon zai zama kamu 25,000 a wajen arewa, fāɗin kuma kamu 10,000 wajen yamma, kamu 10,000 zai zama fāɗinsa a wajen gabas, tsawonsa a wajen kudu zai zama kamu 25,000. A tsakiyarsa ne wuri mai tsarki na Ubangiji zai kasance.

  3. Wannan zai zama na keɓaɓɓun firistoci, zuriyar Zadok, waɗanda suka yi aminci cikin hidimata ba su kuwa karkata kamar yadda Lawiyawa suka yi sa’ad da Isra’ilawa suka karkace ba.

  4. Ba za su sayar da shi ko su musayar da wani sashensa ba. Wannan shi ne mafi kyau na ƙasar ba kuma za a jinginar da ita ga wani ba, gama mai tsarki ce ga Ubangiji.

  5. “Wannan ce ƙasar da za ku raba gādo ga kabilan Isra’ila, kuma wannan ne zai zama rabonsu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  6. “Duk nisan wurare kewaye da birnin zai zama kamu 18,000 ne. “Sunan birnin kuwa daga wannan lokaci zai zama, ‘Ubangiji yana a nan.’ ”

  7. Sai Ubangiji ya bashe Yehohiyakim sarkin Yahuda a hannunsa, tare da waɗansu kayayyakin haikalin Allah. Ya ɗauki waɗannan kayan zuwa cikin haikalin allahnsa a Babilon cikin ma’ajin gidan allahnsa.

  8. Sai Allah ya sa sarkin fada ya nuna masa tagomashi ya kuma ƙaunaci Daniyel,

  9. Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.

  10. Ya roƙe su su roƙi jinƙan Allah na sama domin wannan mafarki, saboda kada a kashe shi da abokansa tare da sauran masu hikima na Babilon.

  11. A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama.

  12. Ya ce, “Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin; hikima da iko nasa ne.

  13. Yana sāke lokuta, yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu. Yana ba da hikima ga masu hikima kuma ilimi ga masu basira.

  14. Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa; ya san abin da yake cikin dare, haske kuwa yana zaune tare da shi.

  15. Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina. Kai ka san hikima da iko, ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”

  16. amma akwai Allahn da yake a sama wanda yake bayyana asirai, ya nuna wa sarki Nebukadnezzar abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayin da ya wuce cikin tunaninka a sa’ad da kake kwance a gadonka su ne,

  17. “A sa’ad da kake kwance, ya sarki, tunaninka ya ga al’amuran da suke zuwa, kuma shi mai bayyana al’amuran ya bayyana maka asiran abubuwan da za su faru.

  18. Ya, sarki, kai ne sarkin sarakuna. Allah na sama ya ba ka iko da girma da suna;

  19. a cikin hannunka ya sanya ɗan adam, da namun jeji da tsuntsayen sama. A duk inda suke zaune, ya maishe ka ka yi mulki a bisansu kai ne kan zinariyan nan na siffar.

  20. “A lokacin mulkin waɗannan sarakunan, Allah na sama zai kafa mulki da ba zai taɓa rushewa ba, ba kuma za a ba ma waɗansu mutane ba. Zai ragargaje waɗannan mulkokin da kuma kawo su ga ƙarshe, amma shi wannan mulki zai dawwama har abada.

  21. Wannan shi ne ma’anar wannan wahayin da ka gani na dutsen da aka yanko daga jikin tsaunin, amma ba da hannun ɗan adam ba, dutsen da ya ragargaza ƙarfen, da tagullar, da yumɓun da azurfar da kuma zinariyar. “Allah mai girma ya nuna wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin gaskiya ne, fassararsa kuma abin dogara ne.”

  22. Sarki ya kuma ce wa Daniyel, “Tabbatacce Allahnka shi ne Allahn alloli da kuma Sarkin sarakuna da mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”

  23. Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”

  24. In an jefa mu cikin tanderun wutar nan, Allahn da muke bauta wa zai iya cetonmu daga ita, kuma ya sarki, zai cece mu daga hannunka.

  25. Sai ya ce, “Ku duba ina ganin mutum huɗu suna tafiya suna yawo a cikin wutar, a sake kuma babu abin da ya same su, na huɗun sai ka ce ɗan alloli.”