Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Za su koyar da mutanena bambanci tsakanin tsarki da rashin tsarki su kuma nuna musu yadda za su bambanta marar tsarki da mai tsarki.

  2. “ ‘A duk wani rashin jituwa, firistoci za su zama alƙalai su kuma yanke magana bisa ga farillaina. Za su kiyaye dokokina da ƙa’idodina a dukan ƙayyadaddun bukukkuwana, su kuma kiyaye Asabbataina da tsarki.

  3. A ranar da ya shiga fili na can ciki na wuri mai tsarki don hidima a wuri mai tsarki, zai miƙa hadaya don zunubi saboda kansa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  4. “ ‘Ni ne kaɗai zan zama abin gādon da firistoci za su kasance da shi. Kada ka ba su wani mallaka a Isra’ila; zan zama mallakarsu.

  5. “ ‘Sa’ad da kuka rarraba ƙasar gādo, ku miƙa wa Ubangiji rabon ƙasar ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa ya zama kamu 25,000 fāɗinsa kuma ya zama 20,000, dukan ƙasar za tă zama mai tsarki.

  6. Zai zama tsattsarkan rabo na ƙasa domin firistoci, waɗanda za su yi hidima a cikin wuri mai tsarki da kuma waɗanda za su zo kusa don su yi hidima a gaban Ubangiji. Zai zama wuri don gidajensu ya kuma zama tsattsarkan wuri saboda wuri mai tsarki.

  7. Wannan fili zai zama mallakarsa a Isra’ila. Kuma sarakunana ba za su ƙara zaluntar mutanena ba amma za su bar gidan Isra’ila ya mallaki ƙasar bisa ga kabilansu.

  8. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko na ce ku sarakunan Isra’ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari’a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  9. A kuma ba da tunkiya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu daga makiyaya da aka yi masa banruwa sosai na Isra’ila. Za a yi amfani da waɗannan don hadayun gari, hadayun ƙonawa da hadayun salama don yin kafara saboda mutane, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  10. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a farkon wata a rana ta fari za ku ba da ɗan bijimi marar lahani a kuma tsarkake wuri mai tsarki.

  11. Kowace rana a kwanaki bakwai na Bikin zai tanada bijimai guda bakwai da raguna bakwai marar lahani a matsayi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da kuma bunsuru saboda hadaya don zunubi.

  12. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a rufe ƙofa ta fili na can cikin da take fuskantar gabas ranaku shida na aiki, amma a ranar Asabbaci da kuma a ranar ganin Sabuwar Wata a buɗe ta.

  13. A Asabbatai da kuma a Sabuwar Wata mutanen ƙasar za su yi sujada a gaban Ubangiji a mashigin wannan hanyar shiga.

  14. Hadaya ta ƙonawar da sarki ya kawo wa Ubangiji a ranar Asabbaci ’yan raguna shida ne da rago guda, dukansu marasa lahani.

  15. “ ‘Sa’ad da mutanen ƙasar suka zo gaban Ubangiji a ƙayyadaddun bukukkuwa, duk wanda ya shiga ta ƙofar arewa don yă yi sujada sai ya fita ta ƙofar kudu; kuma duk wanda ya shiga ta ƙofar kudu sai ya fita ta ƙofar arewa. Ba wanda zai koma ta ƙofar da ya shiga, amma kowa zai fita a ƙofar ɗaura da wadda ya shiga.

  16. Sa’ad da sarki ya ba da hadaya ta yardar rai ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa ce ko hadayun salama ne, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko hadayarsa ta salama yadda yakan yi a ranar Asabbaci. Sa’an nan ya fita, bayan kuma ya fita, sai a rufe ƙofar.

  17. “ ‘Kullum za ku tanada ɗan rago bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji; kowace safiya za ku tanada shi.

  18. Tare da shi za ku tanada hadaya ta gari kowace safiya, da ya haɗa da kashi ɗaya bisa shida na efa tare da kashi ɗaya bisa uku na mai ga garin da aka cuɗa. Miƙawar wannan hadaya ta gari ga Ubangiji dawwammamiyar farilla ce.

  19. “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa in sarkin ya ba wa ɗaya daga cikin ’ya’yansa kyauta daga gādonsa, zai kuwa zama na zuriyar; zai kuwa zama mallakarsu ta wurin gādo.

  20. Kada sarki ya ƙwace gādon mutane, yana korinsu daga mallakarsu. Zai ba wa ’ya’yansa maza gādonsu daga cikin mallakarsa, don kada a raba wani daga mutanena da mallakarsa.’ ”

  21. Ya auna wani kamu dubu, amma a yanzu ruwan ya zama kogin da ban iya hayewa ba, domin ruwan ya taso ya kuma yi zurfin da ya isa a yi iyo a ciki, kogin da ba za a iya hayewa ba.

  22. Sa’ad da na iso can, sai na ga itatuwa masu yawa a kowane gefen kogin.

  23. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Waɗannan su ne iyakokin da za ku raba ƙasar gādo cikin kabilan Isra’ila goma sha biyu, da rabo biyu don Yusuf.

  24. Za ku raba ta daidai a cikinsu. Gama na ɗaga hannu na rantse zan ba da ita ga kakanninku, wannan ƙasa za tă zama gādonku.

  25. A duk kabilar da baƙon yake zama, a can za ku ba shi gādonsa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.