God
Ayoyin da suka ambaci God
“Ku yi maza ku gudu! Ku zauna a kogo masu zurfi, ku da kuke zama a Hazor,” in ji Ubangiji. “Nebukadnezzar sarkin Babilon ya shirya muku maƙarƙashiya; ya ƙulla maƙarƙashiya a kanku.
“Ku tashi ku kuma fāɗa wa al’umma da sauƙi wadda take zama da ƙarfin hali,” in ji Ubangiji, “al’ummar da ba ta da ƙofofi ko ƙyamare; mutanenta suna zama su kaɗai.
Za a washe raƙumansu, garkunansu mai girma za su zama ganima. Zan watsar da waɗanda suke a wurare masu nesa a ko’ina zan kuma kawo musu masifa a kowane gefe,” in ji Ubangiji.
Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Elam, a farkon mulkin Zedekiya sarkin Yahuda.
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ga shi, zan karye ƙarfin Elam, zaunannen ƙarfinsu.
Zan kawo a kan Elam a kusurwoyi huɗu daga kusurwoyi huɗu na duniya; zan watsar da su zuwa kusurwoyi huɗu, kuma ba al’ummar da masu gudun hijirar Elam ba za su kai ba.
Zan ragargaza Elam a gaban maƙiyansu, a gaban waɗanda suke neman ransu; zan kawo masifa a kansu, da zafin fushina,” in ji Ubangiji. “Zan runtume su da takobi sai na kawo ƙarshensu.
Zan sa kursiyina a Elam in kuma hallaka sarkinta da fadawanta,” in ji Ubangiji.
“Duk da haka zan maido da wadatar Elam a kwanaki masu zuwa,” in ji Ubangiji.
Ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Irmiya annabi game da Babilon da kuma ƙasar Babiloniyawa.
“A kwanakin nan, a wannan lokaci,” in ji Ubangiji, “mutanen Isra’ila da mutanen Yahuda gaba ɗaya za su tafi cikin hawaye su nemi Ubangiji Allahnsu.
Za su tambayi hanyar zuwa Sihiyona su kuma juya fuskokinsu wajenta. Za su zo su haɗa kansu ga Ubangiji a madawwamin alkawari da ba za a manta da shi ba.
Duk wanda ya same su ya cinye su; abokan gābansu suka ce, ‘Ba mu da laifi, gama sun yi zunubi wa Ubangiji, wurin kiwonsu na gaske, Ubangiji, abin sa zuciyar kakanninsu.’
Gama zan kuta in kuma kawo a kan Babilon haɗinkan manyan al’ummai na arewa. Za su ja dāgār gāba da ita, kuma daga arewa za a ci ta da yaƙi. Kibiyoyinsu za su zama kamar na gwanayen jarumawa waɗanda ba sa dawowa hannu wofi.
Saboda haka za a washe Babiloniyawa; dukan waɗanda suka washe ta za su ƙoshi,” in ji Ubangiji.
Saboda fushin Ubangiji ba za tă zauna a cikinta ba amma za tă zama kufai gaba ɗaya. Duk waɗanda suka wuce Babilon za su ji tsoro su kuma yi tsaki saboda dukan mikinta.
“Ku ja dāgā kewaye da Babilon, dukanku waɗanda kuke jan baka. Ku harbe ta! Kada ku rage kibiyoyi, gama ta yi zunubi ga Ubangiji.
Ku yi kuwwa a kanta a kowane gefe! Ta miƙa wuya, hasumiyarta ta fāɗi, katangarta sun rushe. Da yake wannan sakayya ce ta Ubangiji, ku ɗauki fansa a kanta; yi mata yadda ta yi wa waɗansu.
Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Zan hukunta sarkin Babilon da ƙasarsa yadda na hukunta sarkin Assuriya.
Amma zan komo da Isra’ila zuwa wurin kiwonsa zai kuwa yi kiwo a Karmel da Bashan; zai ƙosar da marmarinsa a tuddan Efraim da Gileyad.
A kwanakin nan, da kuma a lokacin nan,” in ji Ubangiji, “za a yi bincike don laifin Isra’ila, amma ba za a samu ba, kuma don zunubin Yahuda, amma ba za a sami wani abu ba, gama zan gafarta wa raguwar da na rage.
“Ku fāɗa wa ƙasar Meratayim da waɗanda suke zama a Fekod. Ku fafara, ku kashe kuma hallaka su sarai,” in ji Ubangiji. “Ku aikata dukan abin da na umarce ku.
Na sa miki tarko, Babilon, kika kuwa kamu kafin ki sani; aka same ki aka kuma kama ki domin kin tayar wa Ubangiji.
Ubangiji ya buɗe taskar makamansa ya fitar da makaman fushinsa, gama Maɗaukaki Ubangiji Mai Iko Duka yana da aikin da zai yi a ƙasar Babiloniyawa.
Ku saurari masu gudun hijira da masu neman mafaka daga Babilon suna furtawa a Sihiyona yadda Ubangiji Allahnmu ya ɗauki fansa, fansa domin haikalinsa.