God
Ayoyin da suka ambaci God
“Muddin ina raye,” in ji Sarki, wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki, “wani zai ɓullo wanda yake kamar Tabor a cikin duwatsu, kamar Karmel kusa da teku.
Za su sari kurminta,” in ji Ubangiji, “ko da yake yana maƙare da itatuwa. Sun fi fāra yawa, ba su ƙidayuwa.
Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ina gab da kawo hukunci a kan allahn Amon na Tebes, a kan Fir’auna, a kan Masar da allolinta da sarakunanta, da kuma a kan waɗanda suka dogara ga Fir’auna.
Zan ba da su ga waɗanda suke neman ransu, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da fadawansa. Amma daga baya, Masar za tă kasance da mazauna kamar dā,” in ji Ubangiji.
“Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila. Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nisa, zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yaƙub zai sāke kasance cikin salama, rai kwance, babu kuma wanda zai sa ya ji tsoro.
Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana, gama ina tare da kai,” in ji Ubangiji. “Ko da na hallaka dukan al’ummai sarai inda na kora ka, ba zan hallaka ka sarai ba. Zan hore ka amma da adalci kaɗai; ba zan bar ka ba hukunci ba.”
Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa; za su zama kogi mai rigyawa. Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta, garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu. Mutane za su yi kuka; dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa
Gama rana ta zo da za a hallaka Filistiyawa a kuma datse dukan waɗanda suka ragu waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon. Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa, raguwa daga bakin tekun Kaftor.
“Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji sai yaushe za ka huta? Ka koma kubenka; ka huta, ka yi shiru.’
Amma ta yaya zai huta sa’ad da Ubangiji ya umarta, sa’ad da ya umarta shi don yă faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?”
Game da Mowab. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Kaito ga Nebo, gama za tă lalace. Kiriyatayim za su kunyata a kuma kame ta; katagar za tă sha kunya ta kuma wargaje.
Mai hallakarwa zai aukar wa kowane gari, kuma ba wani garin da zai kuɓuta. Kwari zai lalace tudu kuma ya hallaka, domin Ubangiji ya faɗa.
“La’ananne ne shi wanda yake sake a yin aikin Ubangiji! La’ananne ne wanda ya janye takobinsa daga zub da jini!
Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan aika da mutanen da za su tuntsurar da tuluna, su kuma zubar da ita waje. Za su bar tulunan ba kome a ciki su kuma farfashe tulunanta.
Mowab za tă hallaka a kuma kai wa garuruwanta hari; samarinta kyawawa za su gangara cikin mayanka,” in ji Sarki, wanda sunansa Ubangiji Maɗaukaki ne.
An karye ƙahon Mowab; an karye hannunta,” in ji Ubangiji.
“Ku bugar da ita domin ta tayar wa Ubangiji. Bari Mowab tă yi ta birgima a cikin amanta; bari tă zama abin dariya.
Na san alfarmanta amma a banza ne,” in ji Ubangiji, “kuma taƙamarta ba ya cimma kome.
Saboda haka zan yi kuka a kan Mowab gama dukan Mowab zan yi kuka, Zan yi gurnani don mutanen Kir Hareset.
Zan yi kuka saboda kai, yadda Yazer ya yi kuka Ya kuringar Sibma. Rassanki sun kai har teku; sun kai har tekun Yazer. Mai hallakarwa ya fāɗo a kan ’ya’yan itatuwanku da kuma inabinku da suka nuna.
Farin ciki da murna su ɓace daga lambunan itatuwa da kuma gonakin Mowab. Na dakatar da malalar ruwan inabi daga wurin matsi; ba wanda zai matse su da ihun farin ciki. Ko da yake akwai sowa sowar ba ta farin ciki ba ce.
A Mowab zan kawo ƙarshen waɗanda suke miƙa hadayu a masujadan kan tudu suna kuma ƙone turare ga allolinsu,” in ji Ubangiji.
“Saboda haka zuciyata na makoki don Mowab kamar busa; tana makoki kamar busa saboda mutanen Kir Hareset. Arzikin da suka samu ta ƙare.
A kan dukan rufi a Mowab da kuma a dandalin jama’a babu wani abu sai kuka gama na karye Mowab kamar tulun da babu mai so,” in ji Ubangiji.