God
Ayoyin da suka ambaci God
Har yă zuwa yau ba su ƙasƙantar da kansu ko su nuna bangirma, ko su kiyaye dokata da ƙa’idodin da na sa a gabanku da kakanninku ba.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa na ƙudura in aukar muku da masifa in kuma hallaka dukan Yahuda.
Zan ɗauke raguwar Yahuda waɗanda suka ƙudurta su je Masar su zauna a can. Duk za su hallaka a Masar; za su mutu ta wurin takobi ko su mutu da yunwa. Daga ƙarami zuwa babba, za su mutu ta wurin takobi ko yunwa. Za su zama abin zarge da abin tsoro, abin la’ana da abin ba’a.
Zan hukunta waɗanda suke zama a Masar da takobi, yunwa da annoba, yadda na hukunta Urushalima.
“Ba za mu saurari saƙon da ka yi mana magana a sunan Ubangiji ba!
“Ubangiji bai tuna ya kuma yi tunani game da turaren da aka ƙone a garuruwan Yahuda da kan titunan Urushalima wanda ku da kakanninku, sarakunanku da fadawanku da mutanen ƙasar ba ne?
Sa’ad da Ubangiji bai iya jurewa da mugayen ayyukanku da kuma abubuwa banƙyama da kuka aikata ba, sai ƙasarku ta zama abin la’ana da kufai babu mazauna yadda yake a yau.
Domin kun ƙone turare kuka kuma yi wa Ubangiji zunubi ba ku kuma yi masa biyayya ko ku kiyaye dokarsa ko ƙa’idodinsa ko farillansa ba, wannan masifa ta aukar muku, yadda yanzu kuka gani.”
Sai Irmiya ya ce wa dukan mutane, har da mata, “Ku saurari maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda a Masar.
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku da matanku kun nuna ta wurin ayyukanku abin da kuka yi alkawari sa’ad da kuka ce, ‘Lalle za mu yi abin da muka yi alkawari na ƙone turare da kuma miƙa hadayun sha ga Sarauniyar Sama.’ “To, sai ku ci gaba, ku aikata abin da kuka yi alkawari! Ku cika alkawarinku!
Amma ku ji maganar Ubangiji, dukan Yahudawan da suke zama a Masar, ‘Na rantse da sunana,’ in ji Ubangiji, ‘cewa babu wani daga Yahuda wanda yake zama a ko’ina a Masar zai ƙara kira bisa sunana ko ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji Mai Iko Duka yana raye.”
Gama ina lura da su don lahani, ba alheri ba; mutanen Yahuda da suke a Masar za su hallaka ta wurin takobi da yunwa sai dukansu sun hallaka.
Waɗanda suka kuɓuta wa takobi suka komo zuwa ƙasar Yahuda daga Masar za su zama kima kawai. Sa’an nan dukan raguwar Yahuda waɗanda suka zo don su yi zama a Masar za su san maganar wane ne za tă tabbata, tawa ko tasu.
“ ‘Wannan zai zama alama a gare ku cewa zan hukunta ku a wannan wuri,’ in ji Ubangiji, ‘saboda ku san cewa barazanata ta lahani a kanku tabbatacce za tă cika.’
Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan bayar da Fir’auna Hofra sarkin Masar ga abokan gābansa waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zedekiya sarkin Yahuda ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, abokin gāban da ya nemi ransa.’ ”
“Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana ce maka, Baruk.
Ka ce, ‘Kaitona! Ubangiji ya ƙara baƙin ciki da wahalata; na gaji da nishe-nishe ban kuma huta ba.’ ”
Ubangiji ya ce, “Ka faɗa masa wannan, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan rushe abin da na gina in kuma tumɓuke abin da na dasa, a duk fāɗin ƙasar.
Ya kamata ka nemi manyan abubuwa wa kanka? Kada ka neme su. Gama zan aukar da masifa a kan dukan mutane, in ji Ubangiji, amma duk inda ka tafi zan bar ka ka kuɓutar da ranka.’ ”
Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da al’ummai.
Me nake gani? Sun tsorata, suna ja da baya, an ci jarumawansu. Suna gudu da sauri ba waiwayawa, akwai razana a kowane gefe,” in ji Ubangiji.
Masar tana tashi kamar Nilu, kamar koguna masu tafasa. Tana cewa, ‘Zan tashi in rufe duniya; zan hallakar da birane da kuma mutanensu.’
Amma wannan rana ta Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki ranar ɗaukar fansa, gama ɗaukar fansa a kan maƙiyansa. Takobi zai yi ta ci sai ya gamsu, sai ya kashe ƙishirwansa da jini. Gama Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, zai miƙa hadaya a ƙasar arewa kusa da Kogin Yuferites.
Ga saƙon da Ubangiji ya yi wa Irmiya annabi game da zuwan Nebukadnezzar sarkin Babilon don yă yaƙi Masar.
Me zai sa a wulaƙanta jarumawanka haka? Ba za su iya tsayawa ba, gama Ubangiji zai ture su ƙasa.