Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ko ya gamshe mu ko bai gamshe mu ba, za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu, ga wanda muke aikan ka, saboda ya zama mana da amfani, gama za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu.”

  2. Bayan kwana goma sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya.

  3. Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda kuka aike ni gare shi don in gabatar da kukanku, yana cewa,

  4. ‘In kuka zauna a wannan ƙasa, zan gina ku ba zan kuwa rushe ku ba; zan dasa ku ba kuwa zan tumɓuke ku ba, gama ina baƙin ciki a kan masifar da na aukar a kanku.

  5. Kada ku ji tsoron sarkin Babilon, wanda kuke tsoro a yanzu. Kada ku ji tsoronsa, in ji Ubangiji, gama ina tare da ku zan kuma cece ku daga hannuwansa.

  6. Zan nuna muku jinƙai don yă nuna muku jinƙai ya kuma maido da ku ƙasarku.’

  7. “Amma fa, in kuka ce, ‘Ba za mu zauna a wannan ƙasa ba,’ ta haka kuka kuma nuna rashin biyayya ga Ubangiji Allahnku,

  8. to, ku ji maganar Ubangiji, ya raguwar Yahuda. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In kun ƙudura ku tafi Masar kuka kuma tafi kun zauna a can,

  9. Tabbatacce, duk waɗanda suka ƙudura suka tafi Masar su zauna a can za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba; ba ko ɗayansu zai tsira ko ya kuɓuta wa masifar da zan aukar a kansu.’

  10. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa’ad da kuka tafi Masar. Za ku zama abin la’ana da abin tsoro, abin ƙyama da abin ba’a; ba za ku ƙara ganin wannan wuri ba.’

  11. “Ya ku raguwar Yahuda, Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku je Masar.’ Ku tabbatar da wannan. Na gargaɗe ku yau

  12. cewa in kun yi kuskure sa’ad da kuka aike ni wurin Ubangiji Allahnku kuka kuma ce, ‘Yi mana addu’a ga Ubangiji Allahnmu; ka faɗa mana duk abin da ya faɗa za mu kuwa aikata.’

  13. Na faɗa muku yau, amma har yanzu ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku cikin dukan abin da ya aiko ni in faɗa muku ba.

  14. Sa’ad da Irmiya ya gama faɗa wa mutane dukan maganar Ubangiji Allahnsu, duk abin da Ubangiji ya aike shi ya faɗa musu,

  15. Azariya ɗan Hoshahiya da Yohanan ɗan Kareya da dukan masu ɗaga kai suka ce wa Irmiya, “Kana ƙarya ne! Ubangiji Allahnmu bai aike ka ka ce, ‘Kada ku tafi Masar don ku zauna a can.’

  16. Saboda haka Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da dukan mutane suka yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da su zauna a ƙasar Yahuda.

  17. Saboda haka suka shiga Masar cikin rashin biyayya ga Ubangiji suka tafi har can Tafanes.

  18. A Tafanes maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,

  19. Sa’an nan ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, zan aika wa bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon, zan kuma sa kursiyinsa a kan waɗannan duwatsun da na binne a nan; zai fadada bukkar mulkinsa a bisansu.

  20. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa kun ga masifa mai girmar da na kawo a kan Urushalima da kuma a kan dukan garuruwan Yahuda. A yau sun zama hamada da kuma kango

  21. saboda muguntar da suka aikata. Sun tsokane ni na yi fushi ta wurin ƙone turare da kuma ta wurin bauta wa waɗansu allolin da su ko ku ko kakanninku ba su taɓa sani ba.

  22. Sau da sau na aiki bayina annabawa, waɗanda suka ce, ‘Kada ku yi wannan abin ƙyama da na ƙi!’

  23. Saboda haka, fushina mai ƙuna ya fāɗo a kan garuruwan Yahuda da kuma titunan Urushalima na kuma mai da su kufai da suke a yau.

  24. “To, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa don me kuka kawo irin masifa mai girma haka a kanku ta wurin warewa daga Yahuda maza da mata, yara da jarirai, kun kuma bar kanku babu raguwa?

  25. Me ya sa kuka tsokane ni in yi fushi saboda abin da hannuwanku suka yi, kuna ƙone turare wa waɗansu alloli a Masar, inda kuka zo don ku zauna? Za ku hallakar da kanku ku kuma mai da kanku abin la’ana da abin zargi da abin ba’a a cikin dukan al’umman duniya.