Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. “Ku kira ’yan baka a kan Babilon, dukan waɗanda suke jan baka. Ku yi sansani kewaye da ita duka; kada ku bar wani ya tsira. Ku sāka mata don ayyukanta; ku yi mata yadda ta yi. Gama ta tayar wa Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  2. Saboda haka, samarinta za su fāɗi a tituna; za a kawar da dukan sojojinta a wannan rana,” in ji Ubangiji.

  3. “Ga shi, ina gāba da ke, ya ke mai girman kai,” in ji Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, “gama ranarki ta zo, lokacin da za a hukunta ki.

  4. Mai ɗaga kai za tă yi tuntuɓe ta kuma fāɗi kuma ba wanda zai taimake ta tă tashi; zan hura wuta a garuruwanta da za tă cinye duk waɗanda suke kewaye da ita.”

  5. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “An danne mutanen Isra’ila, haka ma mutanen Yahuda. Dukan waɗanda suka kama su suna riƙe su kankan, suna kin barinsu su tafi.

  6. Duk da haka Mai Fansarsu yana da ƙarfi; Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa. Zai kāre muradunsu gabagadi don yă kawo hutu ga ƙasarsu, amma rashin hutu ga waɗanda suke zaune a Babilon.

  7. “Akwai takobi a kan Babiloniyawa!” In ji Ubangiji “a kan waɗanda suke zama a Babilon da kuma a kan fadawanta da masu hikimarta!

  8. Yadda Allah ya tumɓuke Sodom da Gomorra tare da maƙwabtan garuruwansu,” in ji Ubangiji “haka ma ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.

  9. Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun zuwa wurin kiwo mai dausayi, zan fafare Babilon daga ƙasan nan da nan. Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa domin wannan? Wane ne kamar ni da zai kalubalance ni? Kuma wanda makiyayi zai iya tsaya gāba da ni?”

  10. Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Babilon, abin da ya nufa gāba da ƙasar Babiloniyawa. Za a kwashe ƙananan garkensu a tafi; zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su.

  11. Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan zuga ruhun mai hallakarwa a kan Babilon da mutanen Leb Kamai.

  12. Gama Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila da Yahuda bai yashe su ba, ko da yake ƙasarsu cike da take da laifi a gaban Mai Tsarki na Isra’ila.

  13. “Ku gudu daga cikin Babilon! Bari kowa yă ceci ransa! Kada a hallaka saboda zunubanta. Gama lokaci ne don ramuwar Ubangiji, zai sāka mata bisa ga alhakinta.

  14. Babilon ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji, ta sa dukan duniya ta yi maye. Ƙasashe sun sha ruwan inabinta, saboda haka yanzu sun haukace.

  15. “ ‘Ubangiji ya baratar da mu; zo mu tafi mu yi shelarsa a Sihiyona mu faɗa abin da Ubangiji Allahnmu ya yi.’

  16. “Ku wasa kibiyoyi, ku ɗauko garkuwoyi! Ubangiji ya zuga sarakunan Medes, domin niyyarsa ce yă hallaka Babilon. Ubangiji zai yi ramuwa, zai yi ramuwa saboda haikalinsa.

  17. Ku tā da tuta gāba da katangan Babilon! Ku ƙara matsara, ku kafa masu tsaro, ku shirya kwanto! Ga shi, Ubangiji zai aikata abin da ya faɗa umarninsa a kan mutanen Babilon.

  18. Ubangiji Maɗaukaki ya rantse da zatinsa, ya ce Tabbatacce zan cika ka da mutane kamar fāra, za su kuwa yi sowa don nasara a kanka.

  19. “Ya halicci ƙasa ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa, ya kuma shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.

  20. Sa’ad da ya yi tsawa ruwan da suke sammai sukan yi ruri; yakan sa gizagizai su tashi daga ƙarshen duniya. Yakan tura walƙiya tare da ruwan sama yakan kuma saki iska daga cikin taskokinsa.

  21. Wanda yake na wajen Yaƙub ba kamar waɗannan ba ne, gama shi ne Mahalicci dukan abu, har da kabilar abin gādonsa, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.

  22. “Kai ne kulkin yaƙina, kayan yaƙina, da kai ne na ragargaza ƙasashe, da kai ne na hallaka mulkoki,

  23. da kai ne na ragargaza doki da mahayi, da kai ne na ragargaza keken yaƙin da matuƙi,

  24. da kai ne na ragargaza miji da mata, da kai ne na ragargaza tsoho da saurayi, da kai ne na ragargaza saurayi da budurwa,

  25. da kai ne na ragargaza makiyayi da garke, da kai ne na ragargaza manoma da dawakan noma, da kai ne na ragargaza masu mulki da shugabanni.