God
Ayoyin da suka ambaci God
“Zan sāka wa Babilon da dukan mazaunan Babilon a idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona,” in ji Ubangiji.
“Ga shi, ina gāba da kai, ya ke dutse mai hallakarwa, wadda ta hallaka duniya duka,” in ji Ubangiji. “Zan miƙa hannuna gāba da ke, zan mirgina ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, zan maishe ki ƙonannen dutse.
Ba za a ɗauki dutsen yin kusurwa daga gare ki ba ko na kafa harsashen gini, gama za ki zama marar amfani har abada,” in ji Ubangiji.
Ƙasa ta girgiza tana makyarkyata saboda nufin Ubangiji na gāba da Babilon ya tabbata, nufinsa na mai da ƙasar Babilon kufai don kada kowa yă zauna a can.
Ni Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila na ce, “’Yar Babilon kamar daɓen masussuka a lokacin da ake sussuka, ba da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”
Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “Duba, zan tsaya muku, zan ɗaukar muku fansa, zan sa tekunta kafe in kuma sa maɓulɓulanta su ƙafe.
Amma sa’ad da aka farkar da su, zan yi musu biki in sa su sha su bugu, domin yi sowa da dariya, sa’an nan su shiga barcin da ba za su farka ba,” in ji Ubangiji.
“Zan sauko da su kamar tumaki zuwa mayanka, kamar raguna da bunsurai.
Zan hukunta Bel a Babilon, in sa ya yi aman abin da ya haɗiye. Ƙasashe ba za su ƙara bumbuntowa wurinsa ba. Katangan Babilon kuwa za tă rushe!
“Ku fito daga cikinta, jama’ata! Ku tsere da ranku! Ku tsere daga zafin fushin Ubangiji.
Gama kwanaki tabbatacce suna zuwa, sa’ad da zan hukunta gumakan Babilon, zan kunyatar da dukan ƙasar kuma matattunta duk za su kwanta a cikinta.
Sa’an nan sama da ƙasa da dukan abin da yake cikinsu, za su yi sowa ta murna a kan Babilon, gama daga arewa masu hallakarwa su auko mata,” in ji Ubangiji.
Ku waɗanda kuka tsere wa takobi, ku gudu kada ku tsaya! Ku tuna da Ubangiji a ƙasa mai nesa, ku kuma yi ta tunani a kan Urushalima.”
“Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana kunya ta rufe mu, domin baƙi sun shiga tsarkakan wurare na gidan Ubangiji.”
“Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan hukunta gumakanta, da kuma a dukan ƙasarta waɗanda aka yi wa rauni, za su yi nishi.
Ko da Babilon za tă kai sararin sama ne, ta gina kagaranta mai ƙarfi, duk da haka zan aiki masu hallakarwa a kanta,” in ji Ubangiji.
Gama Ubangiji zai rushe Babilon, zai sa ta ƙame bakinta na alfarma. Sojoji za su yi ta kutsawa kamar raƙuman ruwa; suna tā da muryoyinsu.
Gama mai hallakarwa ya auka wa Babilon, a kama sojojinta, a kuma kakkarya bakkunansu. Gama Ubangiji shi Allah ne mai sakayya; zai yi sakayya sosai.
Zan sa mahukuntanta da masu hikimarta, gwamnoninta, shugabanninta da sojojinta su sha su bugu; za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,” in ji Sarkin, mai suna Ubangiji Maɗaukaki.
Ni Ubangiji Maɗaukaki, na ce, “Za a baje katangan nan na Babilon mai kauri za a kuma ƙone dogayen ƙyamarenta da wuta; mutane sun wahalar da kansu a banza, al’umma sun yi wahala kawai domin wutar lalata.”
Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’
Sa’an nan ka ce, ‘Haka Babilon za tă nutse, ba za tă ƙara tashi ba saboda masifar da zan kawo mata. Mutanenta kuwa za su fāɗi.’ ” Wannan shi ne ƙarshen kalmomin Irmiya.
Sarki Zedekiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehohiyakim ya yi.
Al’amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra’ila da Yahuda, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala. Zedekiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babilon.
Sai ya ƙone haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gine-gine masu alfarman da suke Urushalima.