Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,” shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne? Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne? Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba?

  2. in ba haka ba in Ubangiji ya gani ba zai amince ba ya kuma juye fushinsa daga gare shi.

  3. Ka ji tsoron Ubangiji da kuma sarki, ɗana, kuma kada ka haɗa kai da masu tayarwa,

  4. Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun; a bayyana batun kuwa ɗaukakar sarakuna ne.

  5. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa, Ubangiji kuma zai sāka maka.

  6. Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa.

  7. Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai.

  8. Mai haɗama yakan jawo tā-da-na-zaune-tsaye, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai yi nasara.

  9. Matalauci da azzalumi suna da wannan abu ɗaya. Ubangiji ne yake ba dukansu gani.

  10. Jin tsoron mutum tarko ne, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya.

  11. Mutane sukan nemi samun farin jini daga wurin sarki, amma daga wurin Ubangiji ne mutum kan sami adalci.

  12. Ban koyi hikima ba, ba ni kuma da sani game da Mai Tsarkin nan,

  13. Wane ne ya taɓa haura zuwa sama ya dawo? Wane ne ya tattara iska a tafin hannuwansa? Wane ne ya nannaɗe ruwaye a cikin rigarsa? Wane ne ya kafa dukan iyakokin duniya? Mene ne sunansa, da kuma sunan ɗansa? Faɗa mini in ka sani!

  14. “Kowace maganar Allah ba ta da kuskure; shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.

  15. Kada ka ƙara ga maganarsa, in ba haka ba zai tsawata maka ya kuma nuna kai maƙaryaci ne.

  16. “Abu biyu ina roƙonka, ya Ubangiji; kada ka hana ni kafin in mutu.

  17. In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna.

  18. Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe; amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.

  19. Na dauri aniyata in gwada don in bincika ta wurin hikima dukan abin da ake yi a duniya. Kaya mai nauyi ne Allah ya ɗora a kan mutane!

  20. Ba abin da mutum zai yi da ya fi yă ci, yă sha, yă ji wa ransa daɗi daga aikinsa. Na lura cewa wannan ma, ya fito daga hannun Allah ne,

  21. Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.

  22. Na ga nawayar da Allah ya ɗora a kan mutane.

  23. Ya yi kowane abu da kyau a lokacinsa. Ya kuma sa matuƙa a zukatan mutane, duk da haka sun kāsa gane abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe.

  24. Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.

  25. Na san cewa duk abin da Allah ya yi zai dawwama har abada; ba abin da za a ƙara ko a rage. Allah ya yi haka domin mutane su girmama shi.