Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.

  2. Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne.

  3. Idanun Ubangiji suna a ko’ina, suna lura da masu aikata mugunta da masu aikata alheri.

  4. Ubangiji yana ƙyamar hadayar mugaye, amma addu’ar masu aikata gaskiya kan sa ya ji daɗi.

  5. Ubangiji yana ƙin hanyar mugaye amma yana ƙaunar waɗanda suke neman adalci.

  6. Mutuwa da Hallaka suna nan a fili a gaban Ubangiji, balle fa zukatan mutane!

  7. Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji da a kasance da arziki mai yawa game da wahala.

  8. Ubangiji yakan rushe gidan mai girman kai amma yakan kiyaye iyakokin gwauruwa daidai.

  9. Ubangiji yana ƙyamar tunanin mugaye, amma waɗanda suke da tunani masu tsabta yakan ji daɗinsu.

  10. Ubangiji yana nesa da mugaye amma yakan ji addu’ar adalai.

  11. Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima, kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.

  12. Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke, amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo.

  13. Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi, amma Ubangiji yakan auna manufofi.

  14. Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.

  15. Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa, har ma da mugaye domin ranar masifa.

  16. Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai. Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba.

  17. Ta wurin ƙauna da aminci akan yi kafarar zunubi; ta wurin tsoron Ubangiji mutum kan guji mugunta.

  18. Sa’ad da hanyoyin mutum sun gamshi Ubangiji, yakan sa abokan gāban mutumin ma su zauna lafiya da shi.

  19. ’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu, amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.

  20. Ma’aunai da magwajin gaskiya daga Ubangiji ne; dukan ma’aunai da suke cikin jaka yinsa ne.

  21. Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara, kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji.

  22. Akan jefa ƙuri’a a kan cinya, amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne.

  23. Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya.

  24. Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci, Ubangiji ya ƙi su biyu.

  25. Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi; masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.