God
Ayoyin da suka ambaci God
Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,
da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,
“Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.
Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,
da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,
amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”
Ɗana, in ka yarda da kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,
to, za ka gane tsoron Ubangiji ka kuma sami sanin Allah.
Gama Ubangiji yana ba da hikima, daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya, shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,
gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata yana kuma tsare hanyar amintattunsa.
wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.
Ɗana, kada ka manta da koyarwata, amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka,
Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane.
Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka;
Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,
domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.
Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.
Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi, dukan hanyoyinta kuma salama ne.
Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta; waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.
Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya, ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke;
ta wurin sani aka rarraba zurfafa, gizagizai kuma suka zubo raɓa.
gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.