God
Ayoyin da suka ambaci God
Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi.
La’anar Ubangiji tana a gidan mugaye, amma yakan albarkaci gidan adali.
Yakan yi wa masu girman kai ba’a amma yakan yi wa mai sauƙinkai alheri.
Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji, yana kuma lura da dukan hanyoyinsa.
Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,
Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta; ina ƙin girman kai da fariya, halin mugunta da kuma muguwar magana.
“Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa, kafin ayyukansa na tuntuni;
kafin ya yi duniya ko gonaki ko wata ƙurar duniya.
Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu, sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa,
sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa ya kuma kafa maɓulɓulan zurfafa daram,
sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa domin kada ruwaye su zarce umarninsa, da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya.
A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa. Na cika da murna kowace rana, kullum ina farin ciki a gabansa,
ina farin ciki da dukan duniyarsa ina murna da ’yan adam.
Gama duk wanda ya same ni ya sami rai zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
“Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima, sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa amma yakan lalace burin mugu.
Albarkar Ubangiji kan kawo wadata, ba ya kuma ƙara wahala a kai.
Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai, amma akan gajartar da shekarun mugaye.
Hanyar Ubangiji mafaka ce ga adalai amma lalaci ne ga waɗanda suke aikata mugunta.
Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba, amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.
Ubangiji yana ƙyamar mutane masu muguwar zuciya amma yana jin daɗin waɗanda hanyoyinsu ba su da laifi.
Mutumin kirki kan sami tagomashi daga Ubangiji, amma Ubangiji yakan hukunta mai son yin wayo.
Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya, amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
Wanda tafiyarsa ta aikata gaskiya ce kan ji tsoron Ubangiji, amma wanda hanyoyinsa ba a kan gaskiya ba ne yakan rena shi.
Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka, kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.