Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Bai yi wannan ga wata al’umma ba; ba su san dokokinsa ba. Yabi Ubangiji.

  2. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji daga sammai, yabe shi a bisa sammai.

  3. Yabe shi, dukanku mala’ikunsa, yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.

  4. Yabe shi, rana da wata, yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.

  5. Yabe shi, ku bisa sammai da kuma ku ruwan bisa sarari.

  6. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su.

  7. Ya sa su a wurarensu har abada abadin; ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.

  8. Yabi Ubangiji daga duniya, ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,

  9. walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai, hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,

  10. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka; darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.

  11. Ya tayar wa mutanensa ƙaho, yabon dukan tsarkakansa, na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa. Yabi Ubangiji.

  12. Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka.

  13. Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.

  14. Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.

  15. Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.

  16. Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu,

  17. don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji.

  18. Yabi Ubangiji. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa.

  19. Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa.

  20. Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo,

  21. yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,

  22. yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

  23. Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.

  24. Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye sun rena hikima da horo.

  25. Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina.