Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Women: Unclassified scriptures relating to

113 ayoyi · 47 fannoni

Ayoyi game da Unclassified scriptures relating to

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”

  2. Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama.

  3. Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

  4. Sai mutumin ya ce, “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana nama kuma na namana. Za a ce da ita ‘mace,’ gama an ciro ta daga namiji.”

  5. Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

  6. Sa’an nan ya ce wa macen, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya. Za ki riƙa yin marmarin mijinki zai kuwa yi mulki a kanki.”

  7. Ta haka, sa’ad da aka yi shelar dokar sarki ko’ina a fāɗin masarautarsa, dukan mata za su ba wa mazansu girma, daga ƙarami har zuwa babba.”

  8. Sarki da hakimansa suka gamsu da wannan shawara. Saboda haka sarki ya yi kamar yadda Memukan ya faɗa.

  9. Ya aika da saƙo zuwa ga dukan ɓangarorin masarautar, zuwa ga kowane lardi a irin nasa rubutu, zuwa kuma ga kowane mutane a nasu harshe, ana shelar a kowane yare na mutane, cewa kowane mutum yă zama mai mulki bisa gidansa.

  10. Mace mai hankali na samu bangirma, amma azzalumai za su sami dukiya.

  11. Kamar zinariya a hancin alade haka kyan mace wadda ba ta da hankali.

  12. Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne, amma mace marar kunya tana kama da ciwo a ƙasusuwansa.

  13. Mace mai hikima kan gina gidanta, amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa.

  14. Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.

  15. Wawan yaro lalacin mahaifinsa ne, mace mai yawan faɗa tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.

  16. Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne, amma mace mai basira daga Ubangiji ne.

  17. Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.

  18. Gara a zauna a hamada da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali.

  19. Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.

  20. Mace mai fitina kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa;

  21. hana ta yana kamar yin ƙoƙari tsai da iska ne ko yin ƙoƙarin cafke mai a tafin hannunka.

  22. “Akwai abubuwa uku da duniya kan yi rawan jiki, abubuwa huɗu da ba ta iya jurewa,

  23. bawan da ya zama sarki, wawan da ya ƙoshi da abinci,

  24. macen da ba a ƙauna wadda ta sami miji, da kuma baiwar da ta ɗauki matsayin uwargijiyarta.

  25. Wa yake iya samun mace mai halin kirki? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.