Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Women: First at the sepulcher

23 ayoyi · 47 fannoni

Ayoyi game da First at the sepulcher

  1. Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, sa’an nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin.

  2. Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi.

  3. Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu.

  4. A ranar farko ta mako, da sassafe, bayan fitowar rana, suna kan hanyarsu zuwa kabarin ke nan,

  5. sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?”

  6. Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne.

  7. Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita.

  8. Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi.

  9. Mutane da yawa sosai suka bi shi, a cikinsu ma da mata waɗanda suka yi makoki da kuka dominsa.

  10. Yesu ya juya, ya ce musu, “’Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka saboda ni, amma ku yi kuka saboda kanku, da kuma saboda ’ya’yanku.

  11. Amma dukan mutanen da suka san Yesu, tare da mata da suka bi shi daga Galili, suka tsaya daga nesa suna kallon abubuwan nan.

  12. Matan da suka zo tare da Yesu, daga Galili suka bi Yusuf suka ga kabarin, da kuma yadda aka ajiye jikin.

  13. Sa’an nan, suka koma gida, suka shirya kayan ƙanshi da turare. Amma suka huta a ranar Asabbaci don kiyaye doka.

  14. Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya.

  15. Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin.

  16. Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba.

  17. Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya.

  18. A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu?

  19. Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa,

  20. ‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’ ”

  21. Sai suka tuna da maganarsa.

  22. Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa Sha Ɗayan nan da sauransu, dukan waɗannan abubuwa.

  23. Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su.