Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Women: In business
Ayoyi game da In business
Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa.
Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.
Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.
Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.
Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.
Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.