Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wicked

724 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ga tsarkaka kuwa, kome mai tsarki ne, amma ga waɗanda suke marasa tsarki da kuma marasa ba da gaskiya, ba abin da yake da tsarki. Gaskiya dai, hankulansu da lamirinsu duk marasa tsarki ne.

  2. Sun ɗauka cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna mūsunsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, ba su ma isa su yi aiki nagari ba.

  3. A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna.

  4. Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.

  5. Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji;

  6. Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku.

  7. Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku.

  8. Gama lokaci ya yi da za a fara yi wa iyalin Allah shari’a; in kuwa ya fara da mu, to, me zai faru da waɗanda ba sa biyayya da bisharar Allah?

  9. Kuma, “In da ƙyar masu adalci su kuɓuta, me zai faru da marasa tsoron Allah da kuma masu zunubi?”

  10. Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama;

  11. Amma waɗannan mutane suna yin saɓo a kan abubuwan da ba su fahimta ba. Suna kama da dabbobi marasa hankali, halittun da suke bin abin da jikinsu ya faɗa musu kawai, waɗanda aka haifa don a kama a hallaka, kuma kamar dabbobi su ma za su hallaka.

  12. Za a yi musu sakamako da muguntar da suka yi. A ra’ayinsu jin daɗi shi ne a yi annashuwa da rana tsaka. Su ƙazamai ne marasa kunya, suna cike da jin daɗin sha’awace-sha’awacensu yayinda suke cin biki tare da ku.

  13. Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarrabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi, la’anannun iri!

  14. Sun bar miƙaƙƙiyar hanya suka bauɗe suna bin hanyar Bala’am ɗan Beyor, wanda ya yi ƙaunar hakkin mugunta.

  15. Amma an tsawata masa saboda laifinsa ta wurin jaki, dabbar da ba ta magana, wadda ta yi magana da muryar mutum ta kuma kwaɓi haukan annabin.

  16. Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu.

  17. Gama suna surutai banza na girman kai, ta wurin son bin fasikanci na mutuntaka, sukan jan hankulan mutanen da suke kuɓucewa daga waɗancan masu zama cikin kuskure.

  18. Suna yin musu alkawarin ’yanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi.

  19. In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya.

  20. Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.

  21. Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.

  22. Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi, karya doka ne.

  23. Sai dai kun san cewa Kiristi ya bayyana ne domin yă ɗauke zunubanmu. A cikinsa kuwa babu zunubi.

  24. Ba mai rayuwa a cikinsa da yake cin gaba da yin zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba.

  25. ’Ya’yana ƙaunatattu, kada ku yarda wani yă ruɗe ku. Duk mai yin abin da yake daidai mai adalci ne, yadda Kiristi yake mai adalci.