Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Visions

137 ayoyi · 32 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da kekunan yaƙi dubu ɗaya da ɗari biyu da kuma mahayan dawakai dubu haɗe da mayaƙan Libiyawa, Sukkatawa da kuma Kushawa waɗanda suka wuce ƙidaya suka zo tare da shi daga Masar,

  2. ya ci biranen katanga na Yahuda har zuwa Urushalima.

  3. Ya nemi Allah a kwanakin Zakariya, wanda ya koyar da shi a tsoron Allah. Muddin ya nemi Ubangiji, Allah ya ba shi nasara.

  4. Cikin mafarki da tsakar dare, lokacin kowa yana zurfin barci, na sami saƙon nan.

  5. Tsoro da fargaba suka kama ni har duk ƙasusuwan jikina suka yi ta rawa.

  6. Wani iska ya taɓa mini fuska, sai tsigar jikina ta tashi.

  7. Ya tsaya cik, amma ban iya sani ko mene ne ba. Wani abu ya tsaya a gabana, na kuma ji murya.

  8. Ka taɓa yin magana cikin wahayi, ga mutanenka masu aminci ka ce, “Na ba wa jarumi ƙarfi; na ɗaukaka saurayi daga cikin mutane.

  9. Inda ba wahayi, mutane kan kangare; amma masu albarka ne waɗanda suke kiyaye doka.

  10. A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali.

  11. A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi.

  12. Suna kiran juna, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne; duniya ta cika da ɗaukakarsa.”

  13. Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.

  14. Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”

  15. Sai ɗaya daga cikin serafofin ya yi firiya zuwa wurina tare da garwashi mai wuta a hannunsa, wanda ya ɗiba da arautaki daga bagade.

  16. Da shi ne ya taɓa bakina ya ce, “Duba, wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”

  17. Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?” Sai na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”

  18. Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne.

  19. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Kada ku saurari abin da annabawan suke muku annabci; suna cika ku da sa zuciyar ƙarya. Suna maganar wahayi daga tunaninsu, ba daga bakin Ubangiji ba.

  20. Ƙofofinta sun nutse a cikin ƙasa; ya kakkarya ƙarafanta. Sarakunanta da ’ya’yan sarakunanta duk an kai su bauta cikin waɗansu ƙasashe, babu sauran doka, annabawa kuma ba su samun wahayi daga wurin Ubangiji.

  21. Na duba, sai na ga guguwa ta taso daga arewa babban hadari cike da walƙiya kewaye da haske mai haske sosai. Tsakiyar wutar ta yi kamar ƙarfe mai cin wuta balbal,

  22. a cikin wutar kuwa akwai abin da ya yi kamar halittu guda huɗu. A bayyane kamanninsu ya yi kamar siffar mutum,

  23. amma kowannensu yana da fuskoki huɗu da fikafikai guda huɗu.

  24. Ƙafafunsu miƙaƙƙu ne; kuma ƙafafunsu sun yi kamar na maraƙi suna kuma walƙiya kamar tagullar da aka goge.

  25. A ƙarƙashin fikafikansu huɗu suna da hannuwan mutum a kowane gefe. Dukansu huɗu suna da fuskoki da fikafikai,