Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Holy Trinity

85 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne.

  2. Amma in Kiristi yana a cikinku, jikinku matacce ne saboda zunubi, duk da haka ruhunku yana a raye saboda adalci.

  3. In kuwa Ruhu wannan da ya tā da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya tā da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.

  4. Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa.

  5. Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.

  6. Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa. Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah.

  7. Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah.

  8. Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne;

  9. duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.

  10. Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la’ananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi.

  11. Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne.

  12. Akwai hidimomi iri-iri, amma Ubangiji ɗaya ne.

  13. Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.

  14. Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu,

  15. ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.

  16. Ubangiji fa, shi ne Ruhu, kuma duk inda Ruhun Ubangiji yake, a nan ’yanci yake.

  17. Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba.

  18. Alherin Ubangiji Yesu Kiristi, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.

  19. Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka,

  20. Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “Abba, Uba.”

  21. gama na san cewa ta wurin addu’o’inku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata.

  22. Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa,

  23. Amma dole kullum mu gode wa Allah dominku, ’yan’uwa waɗanda Ubangiji ya ƙaunace, domin daga farko Allah ya zaɓe ku don a cece ku ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu da kuma ta wurin gaskatawa da gaskiya.

  24. Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  25. Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege,