Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Holy Trinity

85 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a ƙauyuka.

  2. “Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.

  3. Sai Yohanna ya ba da wannan shaida, “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa.

  4. Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’

  5. Gama wannan da Allah ya aiko yakan faɗi kalmomin Allah ne, gama Allah yana ba da Ruhu babu iyaka.

  6. Uban yana ƙaunar Ɗan ya kuma danƙa kome a hannuwansa.

  7. Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.

  8. Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada,

  9. Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku.

  10. Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.

  11. “Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni.

  12. Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku.

  13. Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna.

  14. Zai kawo ɗaukaka gare ni ta wurin ɗaukan abin da yake nawa, ya bayyana muku.

  15. Duk abin da yake na Uba nawa ne. Shi ya sa na ce, ‘Ruhun zai ɗauko daga abin da yake nawa, yă bayyana muku.’ ”

  16. Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki.

  17. har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama, bayan ya ba da umarnai ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.

  18. A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai.

  19. Gama Yohanna ya yi baftisma daruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”

  20. An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji.

  21. Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Isra’ila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa.

  22. Kun san abin da ya faru a dukan Yahudiya, farawa daga Galili bayan baftismar da Yohanna ya yi wa’azi,

  23. yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga ko’ina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.

  24. game da Ɗansa. Wanda bisa ga mutuntakarsa, zuriyar Dawuda ne.

  25. Wanda bisa ga Ruhun tsarki, an shaida shi da iko cewa shi Ɗan Allah ne ta wurin tashinsa daga matattu. Wannan bishara kuwa game da Yesu Kiristi Ubangijinmu ne.