- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sin (1)
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Sa’an nan na furta zunubina a gare ka ban kuwa ɓoye laifina ba. Na ce, “Zan furta laifofina ga Ubangiji.” Ka kuwa gafarta laifin zunubina. Sela
Saboda hasalarka babu lafiya a jikina; ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.
Laifofina sun mamaye ni kamar nauyin da ya sha ƙarfin ɗauka.
Na furta laifina; na damu da zunubina.
Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji; bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.
Gama damuwoyin da suka wuce misali sun kewaye ni; zunubaina sun mamaye ni, kuma ba na iya gani. Sun fi gashin kaina yawa, har ma na fid da zuciya.
Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai; ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.”
Ka wanke dukan kurakuraina ka tsarkake ni daga zunubina.
Gama ina sane da laifofina zunubaina kuma kullum suna a gabana.
Kai kaɗai na yi wa zunubi na yi abin da yake mugu a idonka, ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.
Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.
Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba.
Sa’ad da zuciyata ta ɓaci hankalina kuma ya tashi,
na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka.
Zai sāka musu saboda zunubansu yă kuma hallaka su saboda muguntarsu; Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.
Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi; mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta.
Na lura da hanyoyina na kuma mayar da matakaina ga farillanka.
Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba in yi biyayya da umarnanka.
Na kauce kamar ɓatacciyar tunkiya. Ka nemi bawanka, gama ban manta da umarnanka ba.
In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya?
Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu, amma bari ni in zo in wuce lafiya.
za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.
Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.
Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi; igiyoyin zunubinsa za su daure shi kankan.
Zai mutu saboda rashin ɗa’a yawan wawancinsa zai sa yă kauce.