Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sin (1)

240 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba?

  2. Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu,

  3. ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.

  4. Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

  5. Gama ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban kuma isa a kira ni manzo ba, domin na tsananta wa ikkilisiyar Allah.

  6. Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;

  7. bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya,

  8. da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

  9. Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne.

  10. Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.

  11. Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

  12. Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama.

  13. In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu.

  14. In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.

  15. In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.