- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sin (1)
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.
Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu.
Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”
Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”
Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”
Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.”
Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka.
Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”
Sa’an nan ya ce wa macen, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya. Za ki riƙa yin marmarin mijinki zai kuwa yi mulki a kanki.”
Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a la’anta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.
Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za ka kuwa ci ganyayen gona.
Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa, da yake daga cikinta aka yi ka. Gama kai turɓaya ne, kuma ga turɓaya za ka koma.”
Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka.
Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura.
Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.”
Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi.
Bayan da ya kori mutumin, sai ya sa kerubobi da takobi mai harshen wuta yana jujjuyawa baya da gaba a gabashin Lambun Eden don yă tsare hanya zuwa itacen rai.
Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?”
Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa.
Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka.
In ka nome ƙasa, ba za tă ƙara ba ka hatsinta ba. Za ka kuma zama mai yawo barkatai a duniya.”
Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Horon nan ya sha ƙarfina.
Ga shi, yau kana kori na daga ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”
Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci.