Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sciences

74 ayoyi · 13 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  2. Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna,

  3. Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah.

  4. A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.

  5. Dukan waɗannan mutane suna a ƙarƙashin kulawar mahaifansu don kaɗe-kaɗe da bushe-bushe a cikin haikalin Ubangiji, da ganguna, molaye da garayu, don hidima a gidan Allah. Asaf, Yedutun da Heman suna ƙarƙashin kulawar sarki.

  6. Ka kuma ba ɗana Solomon cikakkiyar zuciya don yă kiyaye umarnanka, farillanka da ƙa’idodinka yă kuma yi kome don yă gina ƙasaitaccen gini wanda na riga na yi tanadi dominsa.”

  7. Game da ayyukan mulkin Sarki Dawuda, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin Sama’ila mai duba, tarihin annabi Natan da kuma tarihin Gad mai duba,

  8. sai na fita da dare tare da mutane kalila. Ban faɗa wa wani abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi don Urushalima ba. Ba waɗansu dabbobi kuma tare da ni, sai dai dabbar da na hau.

  9. Da dare na fita ta Ƙofar Kwari wajen Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, ina dudduba katangar Urushalima waɗanda aka rushe da kuma ƙofofinta waɗanda aka ƙone da wuta.

  10. Sa’an nan na ci gaba zuwa wajen Ƙofar Maɓuɓɓuga da kuma Tafkin Sarki, amma babu isashen wuri saboda abin da na hau yă bi;

  11. saboda haka na haura ta kwarin da dad dare, ina dudduba katangar. A ƙarshe, na juya na sāke shiga ta Ƙofar Kwari.

  12. Shugabanni ba su san inda na tafi, ko abin da nake yi ba, domin ban riga na faɗa wa Yahudawa, ko firistoci, ko manyan gari, ko shugabanni, ko sauran waɗanda za su yi aiki, kome ba.

  13. “Na yi tunani cewa, ‘Zan mutu a cikin gidana, kwanakina da yawa kamar turɓayar ƙasa.

  14. “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?

  15. Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?

  16. Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa; su ’yan kasuwa ne a manyan ruwaye.

  17. A wannan rana Ubangiji zai miƙa hannunsa sau na biyu don yă maido da raguwar da ta rage na mutanensa daga Assuriya, daga Masar ta Ƙasa, daga Masar ta Bisa, daga Kush, daga Elam, daga Babiloniya, daga Hamat da kuma daga tsibiran teku.

  18. Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba.

  19. Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai! Bari masananki na taurari su zo gaba, waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata, bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.

  20. Ba magani ne a Gileyad? Ba likita ne a can? To, me ya sa ba warkarwa wa raunin mutanena?

  21. Na ga katanga da ya kewaye filin haikali gaba ɗaya. Tsawon karan awon da yake a hannun mutumin kamu shida ne, sai ya auna kaurin katangar ya sami kamu shida, tsayinta kuma kamu shida.

  22. Sa’an nan ya tafi ƙofar da take fuskantar gabas. Ya hau matakanta ya auna madogarar ƙofa; zurfinta kamu shida ne.

  23. Sai na yi tambaya, na ce, “Ina za ka?” Ya amsa mini ya ce, “Zan je in auna Urushalima, in ga yadda fāɗinta da tsawonta suke.”

  24. Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni.