Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sciences: Mechanics

6 ayoyi · 13 fannoni

Ayoyi game da Mechanics

  1. Saboda haka ka yi wa kanka jirgi da katakon Saifires, ka yi ɗakuna a cikinsa, ka shafe shi da ƙaro ciki da waje.

  2. Ga yadda za ka gina shi; jirgin zai kasance mai tsawon ƙafa 45, fāɗinsa ƙafa 75, tsayinsa kuma ƙafa 45.

  3. Ka yi masa rufi, ka kuma ba da fili inci 18 tsakanin rufin a kowane gefen jirgin. Ka sa ƙofa a gefen jirgin. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe.

  4. Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”

  5. Sai shi da keken yaƙinsa suka shirya, ya kuma ɗauki sojojinsa tare da shi.

  6. Ya ɗauki kekunan yaƙi ɗari shida mafi kyau duka, tare da duk sauran keken yaƙin Masar, da shugabanni kuma a kan dukansu.