Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sanctification

117 ayoyi · 28 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “ ‘Ba za su auri matan da karuwanci ya ɓata su, ko waɗanda mazansu suka sake su ba, gama firistoci masu tsarki ne ga Allahnsu.

  2. An ɗauke su da tsarki, domin suna miƙa abincin Allahnku. An ɗauka su masu tsarki gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, Ni wanda ya mai da ku masu tsarki.

  3. “ ‘In ’yar firist ta ɓata kanta ta wurin zama karuwa, ta kunyatar da mahaifinta ke nan; dole a ƙone ta da wuta.

  4. “ ‘Babban firist, wanda yake ɗaya cikin ’yan’uwansa wanda aka shafe da mai a kansa, wanda kuma aka naɗa don yă sa rigunan firistoci, kada yă bar gashin kansa buzu-buzu, ko ya kyakketa rigunansa.

  5. Ba zai shiga inda akwai gawa ba. Kada yă ƙazantar da kansa, ko ma ta mahaifinsa ce ko ta mahaifiyarsa.

  6. An keɓe shi domina, kada yă ƙazantar da kansa, kada kuwa yă ɓata Tentin Sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce. Ni ne Ubangiji.

  7. “ ‘Dole macen da zai aura ta kasance budurwa.

  8. Ba zai auri matan da mijinta ya mutu, ko macen da mijinta ya rabu da ita, ko macen da ta ɓata kanta ta wurin karuwanci ba, sai dai yă auri budurwa daga cikin mutanensa,

  9. don kada yă ƙazantar da ’ya’yansa a cikin mutanensa. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da shi mai tsarki.’ ”

  10. Ubangiji ya ce wa Musa,

  11. “Faɗa wa Haruna cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, kada ko ɗaya daga cikin zuriyarka, da yake da lahani yă zo kusa domin yă miƙa hadaya ta ci gare ni.

  12. Duk mai lahani, ko makaho, ko gurgu, ko mai naƙasa, ko mai wani lahani a jiki;

  13. ko mai karyayyen ƙafa, ko mai karyayyen hannu,

  14. ko mai ƙusumbi, ko wada, ko wanda yake da lahani a ido, ko mai cuta mai sa ƙaiƙayi, ko mai kirci, ko wanda aka daƙe, ba zai yi kusa domin yă miƙa hadaya ba.

  15. Ba zuriyar Haruna firist, mai lahanin da zai zo kusa don yă miƙa hadayun da aka yi ga Ubangiji da wuta. Da yake yana da lahani, ba zai zo kusa don yă miƙa abincin Allahnsa ba.

  16. Zai iya cin abinci mafi tsarki na Allahnsa, haka ma abinci mai tsarki;

  17. duk da haka saboda lahaninsa, ba zai yi kusa da labule, ko yă yi kusa da bagade don kada yă ƙazantar da wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji wanda yake mai da su masu tsarki.’ ”

  18. “ ‘Firistoci za su kiyaye umarnaina don kada su yi laifi su mutu saboda sun rena su. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da su masu tsarki.

  19. “ ‘In mutum ya miƙa gidansa a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji, firist zai daidaita dacewar ko mai kyau ne, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama.

  20. In mutumin da ya keɓe gidansa ya fanshe shi, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar, gidan kuma zai zama nasa.

  21. “ ‘In wani ya keɓe wa Ubangiji wani sashe daga cikin gonarsa ta gādo, sai yă kimanta kuɗin gonar daidai da yawan irin da za a iya shuka a gonar. Za a kimanta kuɗin a kan shekel hamsin na irin sha’ir.

  22. Ku san cewa Ubangiji ya keɓe masu tsoron Allah wa kansa; Ubangiji zai ji sa’ad da na yi kira gare shi.

  23. “Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka, kafin a haife ka, na keɓe ka; na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.”

  24. Sa’an nan al’ummai za su san cewa Ni Ubangiji na mai da Isra’ila mai tsarki, sa’ad da wuri mai tsarkina yana a cikinsu har abada.’ ”

  25. Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya.