Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sanctification

117 ayoyi · 28 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ga wata magana tabbatacciya, “In muka mutu tare da shi, za mu rayu tare da shi;

  2. In mutum ya tsabtacce kansa daga na farkon zai zama kayan aikin hidima mai daraja, mai amfani ga Maigida, kuma shiryayye domin yin kowane aiki mai kyau.

  3. Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk ’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu ’yan’uwansa.

  4. balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!

  5. Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak.

  6. gama ta wurin hadayan nan guda ɗaya ya kammala har abada waɗanda ake tsarkake.

  7. Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa.

  8. Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yă tsarkake mutane ta wurin jininsa.

  9. yă kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yă aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin.

  10. waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa. Alheri da salama su zama naku a yalwace.

  11. Alheri da salama su zama naku a yalwace ta wurin sanin Allah da Yesu Ubangijinmu.

  12. Ikonsa na Allahntaka ya ba mu kome da muke bukata don rayuwa da kuma tsoron Allah ta wurin sanin wanda ya kira mu ta wurin ɗaukakarsa da nagartarsa.

  13. Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa.

  14. In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.

  15. Yahuda, bawan Yesu Kiristi, ɗan’uwan Yaƙub, Zuwa ga waɗanda aka kira, waɗanda Allah Uba yake ƙauna, waɗanda kuma Yesu Kiristi ya kiyaye.

  16. To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki.

  17. Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.” Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.