Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Religious Zeal

726 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka da muka kāsa daurewa, sai muka ga ya fi kyau a bar mu a Atens mu kaɗai.

  2. Muka aiki Timoti, wanda yake ɗan’uwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yă gina ku yă kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku,

  3. Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba,

  4. ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku.

  5. Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi.

  6. Game da ku kuma ’yan’uwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.

  7. Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.

  8. Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina.

  9. Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

  10. A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami.

  11. Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana.

  12. Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu.

  13. wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba.

  14. Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.

  15. Kai kam, ka san kome game da koyarwata, da halina, da niyyata, bangaskiya, haƙuri, ƙauna, jimiri,

  16. tsanani, shan wahala, irin abubuwan da suka faru da ni a Antiyok, Ikoniyum da kuma Listira, tsananin da na jure. Duk da haka Ubangiji ya cece ni daga dukansu.

  17. wanda ya ba da kansa dominmu don yă fanshe mu daga dukan mugunta yă kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari.

  18. Ka tuna wa mutane su zama masu biyayya ga masu mulki da kuma hukumomi, su zama masu biyayya suna kuma a shirye su yi kowane abin da yake mai kyau,

  19. Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau.

  20. Da a ce suna tunanin ƙasar da suka bari a baya, da sun riga sun sami damar komawa.

  21. A maimako, suna marmarin wata ƙasa mafi kyau, ta sama. Saboda haka Allah ba ya kunya a kira shi Allahnsu, domin ya riga ya shirya musu birni.

  22. Ta wurin bangaskiya ne Musa, sa’ad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Fir’auna.

  23. Ya zaɓa yă sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yă ji daɗin sha’awace-sha’awacen zunubi na ɗan lokaci.

  24. Ya ɗauki wulaƙancin da yake sha saboda Kiristi ya fi dukiyar Masar daraja, domin ya sa ido ga ladansa.

  25. Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba; ya kuwa jure domin ya ga wannan wanda ba a iya gani.