Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Religious Zeal

726 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka, sai mu fita mu je wajensa a bayan sansani, muna ɗaukar kunyar da ya sha.

  2. Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.

  3. Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.

  4. Ku yi mana addu’a. Mun tabbata cewa muna da lamiri mai kyau, kuma muna da marmari mu yi rayuwa ta bangirma a ta kowace hanya.

  5. ’Yan’uwana, in waninku ya kauce daga gaskiya, wani kuma ya komo da shi,

  6. sai yă tuna da wannan. Duk wanda ya komo da mai zunubi daga kaucewarsa, zai cece shi daga mutuwa, yă kuma rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

  7. Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku,

  8. Saboda haka ’yan’uwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba,

  9. za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.

  10. Saboda haka kullum zan tuna muku da waɗannan, ko da yake kun sansu kun kuma kahu ƙwarai cikin gaskiyar da kuke da ita yanzu.

  11. A ganina ya dace in tunashe ku muddin ina raye cikin tentin wannan jiki,

  12. Zan kuwa yi iyakacin ƙoƙari in ga cewa bayan rabuwata kullum za ku iya tuna da waɗannan abubuwa.

  13. Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci;

  14. in har bai ƙyale duniya ta dā ba sa’ad da ya kawo ambaliya a kan mutanenta marasa tsoron Allah, amma ya kiyaye Nuhu, mai wa’azin adalci, da kuma waɗansu bakwai;

  15. Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kuna zuba ido ga wannan, sai ku yi matuƙar ƙoƙari don a same ku ba tabo, sai dai zaman salama da shi.

  16. Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.

  17. Abokina ƙaunatacce, kana da aminci cikin abin da kake yi wa ’yan’uwa, ko da yake su baƙi ne a gare ka.

  18. Sun faɗa wa ikkilisiya game da ƙaunarka. Za ka kyauta in ka sallame su a hanyar da ta cancanci Allah.

  19. Saboda Sunan nan ne suka fito, ba sa karɓan wani taimako daga waɗanda ba masu bi ba.

  20. Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta, in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa mutane masu tsarki na Allah sau ɗaya tak.

  21. Ku ji tausayin waɗanda suke shakka;

  22. ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki.

  23. Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba.

  24. Na yi ta kuka domin ba a iya samun wanda ya cancanta yă buɗe naɗaɗɗen littafin ko yă duba cikinsa ba.

  25. Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Duba, Zakin kabilar Yahuda, da kuma Tushen Dawuda ya ci nasara. Ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin da hatimansa bakwai.”