Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Parents

156 ayoyi · 48 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mutumin ya gaya wa Eli cewa, “Shigowata ke nan daga bakin dāgā. Na kuɓuce daga can yau ɗin nan.” Eli ya ce, “Me ya faru da ’ya’yana?”

  2. Mutumin da ya kawo labarin ya ce, “Isra’ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, mayaƙan kuma sun sha mummunar ɗibga. ’Ya’yanka Hofni da Finehas su ma sun mutu. Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

  3. Da ya ambaci akwatin alkawarin Allah, sai Eli ya fāɗi da baya daga kujeransa kusa da ƙofa, wuyarsa ta karye, ya kuma mutu domin ya tsufa ƙwarai. Ya yi shugabancin Isra’ila shekaru arba’in.

  4. Matar Finehas, ɗansa tana da ciki a lokacin ta kuma kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari cewa an ƙwace akwatin alkawarin Allah, ta kuma labarin surukinta da mijinta sun mutu, sai ta shiga naƙuda, ta kuma haihu. Amma naƙuda ta sha ƙarfinta.

  5. Da tana mutuwa, matan da suke lura da ita suka ce, “Kada ki karaya kin haifi ɗa namiji.” Amma ba tă ba da amsa ko tă kula ba.

  6. Ta ba wa yaron suna Ikabod, ma’ana “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila”, domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma mutuwar surukinta da na mijinta.

  7. Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

  8. Amma Shawulu ya jefe shi da māshi don yă kashe shi. A nan ne Yonatan ya san lalle mahaifinsa ya yi niyya yă kashe Dawuda.

  9. Dawuda ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi, ya kuma shiga gidansa ya kwana kwance a ƙasa.

  10. Sarki ya umarci Yowab, Abishai, da Ittai, ya ce musu, “Ku yi mini hankali da saurayin nan Absalom.” Dukan mutane kuwa suka ji yadda sarki yake ba wa kowane komanda umarni.

  11. Sai gaban sarki ya faɗi. Ya haura zuwa ɗakin da yake kan katangar hanyar shiga ya yi kuka. Yayinda yake tafiya ya ce, “Ya ɗana Absalom! Ɗana, ɗana Absalom! Da ma a ce ni ne na mutu maimakonka. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”

  12. Ba zato sai ya ce wa mahaifinsa, “Wayyo! Kaina yana mini ciwo! Kaina yana mini ciwo!” Sai mahaifinsa ya ce wa bawansa, “Kai shi wurin mahaifiyarsa.”

  13. Bayan bawan ya ɗaga shi ya kai wurin mahaifiyarsa, sai yaron ya zauna a cinyarta har tsakar rana, sa’an nan ya mutu.

  14. “Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. In ka neme shi, za ka same shi; amma in ka yashe shi, zai ƙi ka har abada.

  15. Ka kuma ba ɗana Solomon cikakkiyar zuciya don yă kiyaye umarnanka, farillanka da ƙa’idodinka yă kuma yi kome don yă gina ƙasaitaccen gini wanda na riga na yi tanadi dominsa.”

  16. Shi ma ya yi tafiya a hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ƙarfafa shi yă yi abin da ba shi da kyau.

  17. Ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi.

  18. Bayan lokacin bikin ya wuce, sai Ayuba yă aika su zo don yă tsarkake su. Tun da sassafe zai miƙa hadaya ta ƙonawa domin kowannensu, don yana tunani cewa, “Mai yiwuwa ’ya’yana sun yi wa Allah zunubi, ko sun la’anta shi a cikin zuciyarsu.” Haka Ayuba ya saba yi.

  19. Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar ’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta ’yan’uwansu maza.

  20. Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba; za mu faɗa wa tsara mai zuwa ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji, ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.

  21. Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila, wadda ya umarce kakanni-kakanninmu su koya wa ’ya’yansu,

  22. don tsara na biye su san su, har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba, su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.

  23. Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa, haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;

  24. Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,

  25. ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar; tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.