Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Kings

580 ayoyi · 175 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yoram ya umarta, “Haɗa mini keken yaƙi!” Da aka haɗa, sai Yoram sarkin Isra’ila, da Ahaziya sarkin Yahuda, suka hau suka tafi, kowa a keken yaƙinsa, don su taryi Yehu. Suka sadu da shi a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel.

  2. Sa’ad da Yoram ya ga Yehu sai ya tambaye shi, “Lafiya kuwa ka zo, Yehu?” Yehu ya ce, “Ina kuwa lafiya, da yake dukan bautar gumaka da bokancin mahaifiyarka Yezebel sun bazu ko’ina?”

  3. Yoram ya juya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Cin amana, Ahaziya!”

  4. Sai Yehu ya ja bakansa ya harbi Yoram a tsakanin kafaɗunsa. Kibiyar ta same shi a zuciyarsa sai ya fāɗi a cikin keken yaƙinsa.

  5. Yehu ya ce wa Bidkar, hafsan keken yaƙinsa, “Ka ɗauke shi ka jefar a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel. Ka tuna yadda ni da kai muke a kekunan yaƙi a bayan Ahab mahaifinsa sa’ad da Ubangiji ya yi wannan annabci game da shi,

  6. ‘Jiya na ga jinin Nabot da jinin ’ya’yansa, in ji Ubangiji, kuma ba shakka zan ɗauki fansa a wannan fili, in ji Ubangiji.’ Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar da shi a bisa wannan fegi, bisa ga faɗin Ubangiji. Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar a filin, in ji Ubangiji.”

  7. Sa’ad da Ahaziya sarkin Yahuda ya ga abin da ya faru, sai ya haura hanyar Bet Haggan a guje. Yehu ya bi shi yana ihu, “A kashe shi, shi ma!” Suka ji masa rauni a keken yaƙinsa a hanya zuwa Gur, kusa da Ibileyam amma ya tsere zuwa Megiddo ya mutu a can.

  8. Barorinsa suka ɗauke shi cikin keken yaƙi zuwa Urushalima suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.

  9. (A shekara ta goma sha ɗaya ta Yoram ɗan Ahab, Ahaziya ya zama sarkin Yahuda.)

  10. Da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta shiga hallaka dukan iyalin gidan sarauta.

  11. Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yoram, ’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin ’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi.

  12. Ya kasance a ɓoye, shi da mai lura da shi, a haikalin Ubangiji shekara shida yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.

  13. A shekara ta ashirin da uku ta Yowash ɗan Ahaziya, sarkin Yahuda, Yehoyahaz ɗan Yehu, ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuwa yi mulki shekaru goma sha bakwai.

  14. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji ta wurin bin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, bai kuwa guje musu ba.

  15. Saboda haka fushin Ubangiji ya ƙuna a kan Isra’ila, kuma da daɗewa ya sa su a ƙarƙashin ikon Hazayel sarkin Aram da Ben-Hadad ɗansa.

  16. Sai Yehoyahaz ya nemi tagomashin Ubangiji, Ubangiji kuwa ya saurare shi, domin ya gan irin matsin da sarkin Aram yake yi wa Isra’ila.

  17. Sai Ubangiji ya tā da mai ceto wa Isra’ila, suka kuma kuɓuta daga ikon Aram. Ta haka Isra’ilawa suka yi zama a gidajensu yadda suka yi a dā.

  18. Sai dai ba su bar yin zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa Isra’ila ta aikata; suka ci gaba da yinsu. Haka ma, ginshiƙin Ashera ta kasance a tsaye a cikin Samariya.

  19. Ba abin da ya rage na rundunar Yehoyahaz sai mahayan dawakai hamsin, kekunan yaƙi goma da kuma sojoji ƙasa dubu goma. Gama sarkin Aram ya hallaka sauran, ya kuma yi kaca-kaca da su kamar ƙura a masussuka.

  20. Game da sauran ayyukan mulkin Yehoyahaz, dukan abubuwan da ya yi da kuma nasarorinsa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

  21. Yehoyahaz ya huta da kakanninsa, aka binne shi a Samariya, Yehowash ɗansa kuma ya gāje shi.

  22. A shekaru talatin da bakwai ta Yowash sarkin Yahuda, Yehowash ɗan Yehoyahaz ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki shekaru goma sha shida.

  23. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, bai juya ga barin zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, ya ci gaba da yinsu.

  24. Game da sauran ayyukan mulkin Yowash, da dukan abubuwan da ya yi, da kuma nasarorinsa, haɗe da yaƙin da ya yi da Amaziya sarkin Yahuda, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

  25. Yowash ya huta da kakanninsa, Yerobowam kuwa ya gāje shi. Aka binne Yehowash a Samariya tare da sarakunan Isra’ila.