Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Doubting

105 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Raina yana baƙin ciki a cikina; saboda haka zan tuna da kai daga ƙasar Urdun, a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar.

  2. Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.

  3. Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya.

  4. Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka.

  5. Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni

  6. sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.

  7. “Ubangiji zai ƙi ne har abada? Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba?

  8. Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada? Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci?

  9. Allah ya manta yă yi jinƙai? Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?” Sela

  10. Ya Yaƙub, ya Isra’ila, me ya sa kake ce kana kuma gunaguni cewa, “Hanyata tana a ɓoye daga Ubangiji; Allah bai kula da abin da yake damuna ba”?

  11. Ba ku sani ba? Ba ku ji ba? Ubangiji madawwamin Allah ne, Mahaliccin iyakokin duniya. Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba, kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.

  12. Amma Sihiyona ta ce, “Ubangiji ya yashe ni, Ubangiji ya manta da ni.”

  13. “Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa? Mai yiwuwa ta manta, amma ba zan taɓa manta da ke ba!

  14. “Duba yadda aka gina mahaurai don a kame birni. Saboda takobi, yunwa da annoba, za a ba da birnin ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye shi da yaƙi. Abin da ka faɗa ya faru, yadda kake gani yanzu.

  15. Ko da yake za a ba da birnin ga Babiloniyawa, kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka ce mini, ‘Saye fili da azurfa ka kuma sa a shaida cinikin.’ ”

  16. Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi.

  17. Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.

  18. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”

  19. Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

  20. Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”

  21. Sa’ad da Yohanna Mai Baftisma ya ji a kurkuku abin da Kiristi yake yi, sai ya aiki almajiransa

  22. su tambaye shi, “Kai ne wanda zai zo, ko kuwa mu sa ido ga wani?”

  23. Ya ce, “Zo.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu.

  24. Amma da ya ga haukar iskar, sai ya ji tsoro, ya kuma fara nutsewa, sai ya yi ihu ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”

  25. Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”