Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Doubting: General references

31 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Ka tuna yadda ka yi wa mutane da yawa magana, yadda ka ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi.

  2. Maganarka ta ƙarfafa waɗanda suka yi tuntuɓe; ka ƙarfafa gwiwoyin da suka rasa ƙarfinsu.

  3. Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya; wahala ta sa ka rikice.

  4. Ashe bai kamata ka dogara ga Allahnka ba, amincinka kuma yă zama begenka?

  5. Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba.

  6. Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili.

  7. Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba.

  8. In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne! In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa?

  9. Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi; in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi.

  10. “Ko da yake ba ni da laifi, ban damu da kaina ba; na rena raina.

  11. Ba bambanci; shi ya sa na ce, ‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’

  12. Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi.

  13. Shi ya sa na tsorata a gabansa; sa’ad da na yi tunanin wannan duka, nakan ji tsoronsa.

  14. Allah ya sa zuciyata ta yi sanyi; Maɗaukaki ya tsorata ni.

  15. Duk da haka duhun bai sa in yi shiru ba, duhun da ya rufe mini fuska.

  16. “Na yi kuka gare ka ya Allah, amma ba ka amsa mini ba. Na tashi tsaye, amma sai ka dube ni kawai.

  17. Ka dube ni ba tausayi; Ka kai mini hari da ƙarfin hannunka.

  18. Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna.

  19. Raina yana baƙin ciki a cikina; saboda haka zan tuna da kai daga ƙasar Urdun, a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar.

  20. Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.

  21. Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya.

  22. Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka.

  23. Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni

  24. sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.

  25. “Ubangiji zai ƙi ne har abada? Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba?