Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Commerce

82 ayoyi · 64 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ya kwantar da hadiri suka yi tsit; raƙuman ruwan teku suka yi shiru.

  2. Suka yi murna sa’ad da wuri ya kwanta, ya kuma bishe su zuwa inda suka so su kai.

  3. Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa.

  4. Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.

  5. Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.

  6. Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.

  7. Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.

  8. Yayinda suke kuka a kanki kuwa, za su yi makoki dominki suna cewa, “Wa ya taɓa yin shiru kamar Taya, kewaye da teku?”

  9. Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi, kin gamsar da al’ummai masu yawa; da dukiyarki masu yawa da kuma kayan cinikinki kin azurtar da sarakunan duniya.

  10. Yanzu teku ta farfashe ki cikin zurfafan ruwaye; kayan cinikinki da dukan kamfaninki sun nutse tare da ke.

  11. Dukan mazaunan bakin teku sun giggice saboda masifarki; sarakunansu sun tsorata ƙwarai fuskokinsu kuwa sun yamutse don tsoro.

  12. ’Yan kasuwa a cikin al’ummai suna yin miki tsaki; kin zo ga mummunar ƙarshe ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ”

  13. Ta wurin yawan kasuwancinka ka cika da rikici, ka kuma yi zunubi. Saboda haka na kore ka da kunya daga dutsen Allah, na kore ka, ya kerub mai tsaro, daga cikin duwatsun wuta.

  14. Zuciyarka ta cika da alfarma saboda kyanka, ka kuma lalace hikimarka saboda darajarka. Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa; na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna.

  15. Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka. Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suke kallonka.

  16. Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”

  17. Sai na ji wata murya daga sama ta ce, “Ku fita daga cikinta, mutanena, don kada zunubanta su shafe ku, don kada wata annobarta ta same ku;

  18. gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama. Allah kuma ya tuna da laifofinta.

  19. Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku; ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi. Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata.

  20. Ku ba ta isashen azaba da baƙin ciki kamar daraja da kuma jin daɗin da ta ba wa kanta. A zuciyarta takan yi taƙama, ta ce, ‘Ina zama kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taɓa yin makoki ba.’

  21. Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata, mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta zai cinye ta, gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shari’anta ta.

  22. “Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita.

  23. Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma. Ya ke Babilon, birni mai iko! Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’

  24. “Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu

  25. kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi;