Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Commerce: Denunciations connected with abuses of

8 ayoyi · 64 fannoni

Ayoyi game da Denunciations connected with abuses of

  1. Yayinda suke kuka a kanki kuwa, za su yi makoki dominki suna cewa, “Wa ya taɓa yin shiru kamar Taya, kewaye da teku?”

  2. Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi, kin gamsar da al’ummai masu yawa; da dukiyarki masu yawa da kuma kayan cinikinki kin azurtar da sarakunan duniya.

  3. Yanzu teku ta farfashe ki cikin zurfafan ruwaye; kayan cinikinki da dukan kamfaninki sun nutse tare da ke.

  4. Dukan mazaunan bakin teku sun giggice saboda masifarki; sarakunansu sun tsorata ƙwarai fuskokinsu kuwa sun yamutse don tsoro.

  5. ’Yan kasuwa a cikin al’ummai suna yin miki tsaki; kin zo ga mummunar ƙarshe ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ”

  6. Ta wurin yawan kasuwancinka ka cika da rikici, ka kuma yi zunubi. Saboda haka na kore ka da kunya daga dutsen Allah, na kore ka, ya kerub mai tsaro, daga cikin duwatsun wuta.

  7. Zuciyarka ta cika da alfarma saboda kyanka, ka kuma lalace hikimarka saboda darajarka. Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa; na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna.

  8. Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka. Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suke kallonka.