Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ammonites

135 ayoyi · 11 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa.

  2. Dukan al’ummai za su bauta masa da ɗansa da kuma jikansa har sai har lokacin ƙasarsa ya kai; sa’an nan al’ummai masu yawa da kuma manyan sarakuna za su kasance a ƙarƙashinsa.

  3. “ ‘ “Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa.

  4. Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’

  5. Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka.

  6. Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.” ’ ”

  7. Game da Ammonawa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Isra’ila ba shi da ’ya’ya maza ne? Ba shi da magāda ne? To, me ya sa Molek ya mallaki Gad? Me ya sa mutanensa suka zama a garuruwansa?

  8. Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi kirarin yaƙi a kan Rabba ta Ammonawa; zai zama tarin juji, za a sa wuta a ƙauyukan da suke kewayenta. Sa’an nan Isra’ila zai kori waɗanda suka kore shi,” in ji Ubangiji.

  9. “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama an hallaka Ai! Ku tā da murya ku yi kuka, ya mazaunan Rabba! Ku sa tufafin makoki; ku ruga nan da can a cikin katanga, gama Molek zai tafi bauta, tare da firistocinsa da kuma fadawansa.

  10. Me ya sa kuke taƙama da kwarurukanku, taƙama da kwarurukanku masu amfani? Ya ke diya marar aminci, kin dogara a wadatarki kika kuma ce, ‘Wa zai iya fāɗa mini?’

  11. Zan kawo razana a kanki daga waɗanda suke kewaye da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Za a kore kowannenku, babu wani da zai tattara masu gudun hijira.

  12. “Duk da haka, daga baya, zan maido da wadatar Ammonawa,” in ji Ubangiji.

  13. “Kai kuma, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da Ammonawa da kuma zarginsu. “ ‘Takobi, takobi, an ja don kisa, an goge don cinyewa yana haske kamar walƙiya!

  14. Duk da wahayin ƙarya game da kai, duban ƙarya game da kai, za a sa shi a wuyan mugaye waɗanda za a kashe, waɗanda kwanansu ta zo, waɗanda lokacin hukuncinsu ya cika fal.

  15. “ ‘Ka mai da takobi a kubensa. A inda aka halicce ka, a ƙasar kakanninka, zan hukunta ka.

  16. Zan zub da hasalata a kanka in hura maka wutar fushina; Zan ba da kai a hannun mugayen mutanen da suka gwanince a hallakarwa.

  17. Za ka zama itacen wuta, za a zub da jininka a ƙasarka, ba za a ƙara tuna da kai ba; gama Ni Ubangiji na faɗa.’ ”

  18. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  19. “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa ka kuma yi annabci a kansu.

  20. Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun ce “Yauwa” a kan wuri mai tsarkina sa’ad da aka ƙazantar da shi da kuma a kan ƙasar Isra’ila sa’ad da aka mai da ita kufai da lokacin da aka kai mutanen Yahuda bautar talala,

  21. saboda haka zan ba da ku ga mutanen Gabas abin mallaka. Za su kafa sansanoninsu su yi tentunansu a cikinku; za su ci ’ya’yan itatuwanku su kuma sha madararku.

  22. Zan mai da Rabba wurin kiwo don raƙuma, Ammon kuma wurin hutu don tumaki. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.

  23. Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun tafa hannuwanku kuka kuma buga ƙafafunku, kuna farin ciki don nuna dukan ƙiyayyarku a kan ƙasar Isra’ila,

  24. saboda haka zan miƙa hannuna gāba da ku in kuma ba da ku ganima ga al’ummai. Zan datse ku daga al’ummai in kuma kore ku daga ƙasashe. Zan hallaka ku, za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  25. “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Mowab da Seyir sun ce, “Duba, gidan Yahuda ta zama sauran al’ummai,”